Arsene Wenger: Tsohon kocin Arsenal ya ce zai kai wa kulub ɗin ziyara 'wata rana'

Arsene Wenger

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Arsene Wenger ne kocin da ya fi daɗewa a Arsenal kuma wanda ya fi samun nasarori daga 1996 zuwa 2018

Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce a shirye yake ya koma kulob ɗin 'wata rana' bayan ɗauke ƙafarsa tun da ya bar Emirates shekara biyu da suka gabata.

Wenger mai shekara 70, ya ajiye aikinsa a Mayun 2018 bayan taimaka wa Gunners lashe kofin Premier uku da kofin FA bakwai a shekara 22 da ya shafe a ƙungiyar.

An sha gayyatarsa amma ya ce ya fi kyau ya ɗauke ƙafarsa gaba ɗaya daga kulob ɗin bayan ya tafi.

"Na ga ya fi kyau na sa ido daga nesa," kamar yadda ya shaida wa The Times.

Wenger ya bayyana barinsa Arsenal a matsayin "babban kaɗaici rabuwa marar daɗi" kuma yanzu ba shi da "wata alaƙa da kulub ɗin."

Hakan ya saɓa da abin da aka saba gani cikin masu horar da 'ƴan wasan da suka fi daɗewa a Premier kamar Sir Alex Ferguson, wanda aka bai wa matsayi a hukumar gudanarwar Manchester United lokacin da ya yi ritaya a 2013.

Wenger ya ce bai san dalilin da ya sa ba a ba shi wani muƙami ba a Arsenal, amma ya ce zai karɓa idan da ya samu damar.

"Na sha faɗa cewa akwai rawar da zan iya takawa a kulub din, amma na fahimci da farko cewa ya fi dacewa mu yi nesa da juna," in ji shi.

A baya Wenger ya ce yana son ya dawo aikin horar da 'ƴan wasa a farkon 2019, amma maimakon haka sai ya karɓi muƙamin da Fifa ta ba shi a watan Nuwamban 2019 na shugaban bunƙasa ƙwallon ƙafa a duniya.

Yanzu Wenger ya ce ba shi da tabbas ko zai dawo horar da 'ƴan wasa.

"Shekara 40 abin da nake yi kenan kowace rana a rayuwata, yanzu ina yin wasu wasannin. Ina ziyartar dangina da 'ƴan uwa da abokan arziki. Ina karatu sosai. Ina more rayuwata sosai."