Kante ya koma atisaye bayan tsoron cutar korona

Ngolo Kante

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Talata dan wasan Chelsea, N'Golo Kante ya fara atisaye a shirin da kungiyar take na ci gaba da gasar Premier a mako mai zuwa.

Za a ci gaba da wasannin Premier League ranar 17 ga watan Yuni da wasa tsakanin Aston Villa da Sheffield United da na Manchester City da Arsenal.

Tun farko Chelsea ta bai wa Kante hutu tun bayan da dan kwallon tawagar Faransa ya bayyana tsoro kan matakan lafiyarsa dangane da bullar cutar korona.

Kawo yanzu dan wasan hankalinsa ya kwanta ya kuma koma atisaye domin bayar da gudunmawar da zai bai wa Chelsea ta kare cikin 'yan hudun farko a gasar Premier ta shekarar nan.

Saura wasa 92 a karkare gasar Premier League ta 2019-20, kuma Chelsea za ta fafata da Aston Villa ranar 21 ga watan Yuni.

Chelsea tana mataki na hudu a kan teburin gasar bana da tazarar maki uku tsakaninta da Manchester United ta biyar kuma saura wasanni tara da kowacce kungiya za ta buga.