Ba a sanar da filin da za a kara a wasan Everton da Liverpool ba

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Juma'a ake sa ran fayyace filin da za a kara a wasan hamayya tsakanin Everton da Liverpool idan an ci gaba da wasannin Premier League na bana.

Ranar 12 ga watan Yuni kungiyoyin za su fafafata a wasa na hamayya ko dai a gidan Everton ko kuma a wani fili na daban a karawar da ake kira ta Merseyside.

Wasan na Everton da Liverpool na daga cikin guda biyu da hukumar gudanar da Premier League ta fitar da jadawali ranar Juma'a ba tare da fayyace filin da za a yi gumurzu ba.

Daya karawar ita ce tsakanin Manchester City da Liverpool da za su kece raini ranar 2 ga watan Yuni.

Everton dai a shirye take ta karbi bakuncin Liverpool wadda za ta iya lashe kofin Premier a ranar idan Arsenal ta ci Manchester City ranar 17 ga watan Yuni.

Ko kuma ta daga kofin Premier na shekarar nan a Anfield a wasan da za ta yi da Crystal Palace ranar 24 ga watan Yuni.

Cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasannin tamaula a Ingila don gudun yada cutar korona.

Liverpool ce ke kan gaba a teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City, kuma karon farko da za ta ci kofin Premier League tun bayan shekara 30.