Barayi sun kwashe wa Dele Alli gwala-gwalai

Asalin hoton, Getty Images
'Yan fashi rike da wuka sun shiga gidan dan kwallon Tottenham, Dele Alli inda suka kwashe masa dukiya.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba da asuba, inda mutum biyu maza suka shiga gidan dan kwallon Ingilar a yankin arewacin London.
Barayin sun yi wa Alli barazana da wuka sannan suka nushe shi - a yayin da ya ji rauni a fuskarsa.
Barayin sun yi awon gaba da gwala-gwalai kafin su tsere.
A halin yanzu dai, Alli ya mika wa 'yan sanda bidiyon CCTV na lamarin.






