Sane zai koma Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Manchester City dan kasar Jamus Leroy Sane, mai shekara 24, na dab da komawa Bayern Munich, wacce za ta saye shi a kan £70m.(Mirror)
Kungiyoyin Gasar Premier za su gana ranar Juma'a domin tattaunawa kan ko za a kammala kakar wasa ta bana zuwa ranar 30 ga watan Yuni. Idan aka kada kuri'a kan batun, dole kungiyoyi 14 cikin 20 su amince kafin a dauki matakin. (Guardian)
Dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Kai Havertz, mai shekara 20, ya ce a shirye yake ya koma wata kasar waje, inda aka ce Liverpool na cikin kungiyoyin Premier da ke son dauko shi.(Sport Bild - in German)
A shirye dan wasan Chelsea da Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, yake ya amince a rage albashinsa domin ya samu damar komawa Inter Milan a bazara. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Dan wasan Manchester United da Argentina Marcos Rojo, mai shekara 30, yana son tsawaita zaman aron da yake yi a kungiyar da ke kasarsa Estudiantes saboda sau daya kacal ya buga mata wasa - sakamakon raunin da ya yi da kuma dakatar da kakar wasa saboda cutar korona (Manchester Evening News)
AC Milan ta yanke shawarar fasa shirin da take yi na dauko dan wasan tsakiya na Ingila Adam Lallana a bazara. Kwantaragin tsohon dan wasan na Southampton, mai shekara 31, ya kare a Liverpool a karshen watan Yuni (Mirror)
Arsenal za ta iya yin amfani da damar da take da ita kan dan wasan Faransa Alexandre Lacazette a karshen kakar wasan bana, a yayin da Atletico Madrid ta bayyana sha'awar sayen dan wasan mai shekara 28. (AS - in Spanish)
Sai dai Arsenal ka iya rasa dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, wanda Real Madrid take son sayo shi. Zinedine Zidane yana son dauko dan wasan mai shekara 30 a matsayin zabin da ya rage masa kan dan wasan Inter Milan Lautaro Martinez - wanda yake son komawa Barcelona. (Sport - in Spanish)
Dan wasan Leicester dan kasar Austria Christian Fuchs, mai shekara 34, yana tsaka-mai-wuya a kan ko ya tsawaita zamansa a King Power Stadium ko kuma ya koma Amurka domin sake ganawa da iyalansa. (Daily Mail)
Golan Liverpool Loris Karius ya ce har yanzu yana tattaunawa da Jurgen Klopp bayan da ya kammala zaman aro a kungiyar Besiktas ta Turkiyya ko da yake bai san inda zai koma ba. Dan kasar ta Jamus, mai shekara 26, yana da kwangila a Anfield wacce ba za ta kare ba sai 2022. (Sky Sports)











