Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier League: Everton ta doke Crystal Palace
Everton ta ci wasa na biyar a jere ba tare da an doke ta ba bayan ta casa Crystal Palace da ci 3-1 a filin wasa na Goodison Park.
Mai masaukin bakin, Everton, ce ta mamaye minti 45 na farkon wasan kuma tun a minti na 18 ta fara jagorancinsa bayan Bernard ya jefa kwallo a raga.
Crystal Palace, wadda har yanzu ba ta ci wasa ba a 2020, ta yunkura ta farke ta kafar Christian Benteke bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Daga nan kuma Everton ta jure hare-haren da Palace ta rika kai mata har ta kara ta biyu a minti na 58, yayin da Richarlison ya ratsa bayan Palace kuma ya cilla ta a gidan kifinsu.
Mai tsaron ragar Everton, Jordan Pickford, ya yi kokarin kare wata kwallon Benteke daga shiga raga, kafin dga bisani Calvert-Lewin ya kara ta uku.
Nasarar ta sa Everton ta koma ta shida da tazarar maki daya tsakaninta da Tottenham, wadda ke mataki na biyar da kuma kwantan wasa daya.
Ita kuwa Palace tana ta 14, maki shida tsakaninta da 'yan ukun kasan teburi, wadanda baki dayansu suke da kwantan wasa.