Dan wasan Man City Raheem Sterling zai yi jinyar 'makonni'

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce dan wasan gaba na kulob din Raheem Sterling zai yi jinyar "makonni" saboda raunin da ya yi a cinyarsa.

An dauke dan wasan dan kasar Ingila, mai shekara 25, daga filin wasa lokacin da ya rika dingishi a fafatawar da Tottenham ta doke su da ci 2-0 ranar Lahadi.

"Zai kwashe makonni yana jinya, ko da yake a yanzu haka ban san tsawon lokacin da zai yi ba ya wasa ba," in ji Guardiola.

City na matsayi na biyu a saman teburin gasar Firimiya, inda suke da maki 22 a bayan kungiyar da ke matsayi na daya Liverpool.

Kocin ya tabbatar cewa binciken ya nuna cewa ya yi raunin ne a cinyarsa ta hagu.

Sterling ya buga wasa 23 cikin gasa 25 da City ta fafata a kakar wasa ta bana.

"Rashinsa matsala ce amma a farkon kakar wasa ba ma tare da Gundo [Ilkay Gundogan] da kuma ([Aymeric] Laporte a wannan kakar. Don haka za mu yi amfani da sandar da ke hannunmu," a cewar Guardiola.

Sai dai akwai labari mai faranta rai game da dan wasan City Leroy Sane, wanda ya fara atisaye bayan ya yi fama da jinyar gwiwarsa a fafatawar da suka yi da Liverpool a gasar Community Shield ranar hudu ga watan Agusta.

Kocin City ya kara da cewa "Ya soma atisaye da mu. Yana bukatar murmurewa kafin ya shiga gasa. Yana bukatar lokaci. Yana bukatar makonni."