Boksin: Buhari ya yaba wa Anthony Joshua

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yaba wa zakaran damben Boksin na duniya ajin masu nauyi, Anthony Joshua, bisa nasarar da ya samu kan Andy Ruiz ranar Asabar da dare.

Mahaifiyar Anthony Joshua, Yeta da kuma mahaifinsa Robert Joshua 'yan asalin Najeriya ne duk da cewa an haife shi ne a Watford ta kasar Ingila.

"Na jinjina wa zakaran Boksin Anthony Joshua bisa nasarar da ya samu a daren Asabar kan Andy Ruiz Jnr," Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter.

"Ka saka farin ciki a zukatan miliyoyin 'yan Najeriya a gida da kuma waje. Muna matukar alfahari da kai yanzu da kuma nan gaba," in ji Shugaban.

Anthony Joshua ya kwato kambunsa na IBF da WBA da kuma na WBO wanda Ruiz ya kwace daga hannunsa wata shida da ya gabata a New York.

An yi damben ne a Diriyah Arena a birnin Riyad na Saudiyya a gaban 'yan kallo sama da 14,000.

Yanzu Joshua, mai shekara 30, ya shiga tarihin 'yan damben boksin na duniya da suka taba kare kambun zakaran damben duniya ajin masu nauyi, wadanda da suka hada da Muhammad Ali da Lennox Lewis da Evander Holyfield da Mike Tyson da Floyd Patterson.

Ga yadda Anthony Joshua ya dambace Andy Ruiz