El Clasico: Madrid ta ce Hazard ya yi tsagewar kashi

Eden Hazard

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hazard ya ji rauni ne sakamakon ketar da Thomas Meunier ya yi masa a wasan Champions League

Babu tabbas ko tauraron dan wasan gaban Real Madrid Eden Hazard zai buga wasan hamayya na El Clasico tsakan Madrid din da Barcelona bisa raunin da ya ji a karawarsu da PSG.

Hazard ya ji raunin ne biyo bayan ketar da abokin wasansa a kasar Belgium, Thomas Meunier ya yi masa a wasan Zakarun Turai ranar 26 ga watan Nuwamba.

Tun farko mai horarwa Zinediune XZidane ya yi fatan raunin ba wani babba ba ne.

"Ina fatan zai warke idan ya samu hutun kwana uku. Za mu gani dai, ina fatan ba wani babbar rauni ba ne," in ji Zidane, jim kadan bayan tashi daga wasan.

Sai ga shi a yau Real Madrid ta fitar da sanarwa cewa an gano sabuwar matsala game da raunin da ya ji.

"Bayan gwaje-gwajen da aka yi kan dan wasanmu, Eden Hazard, har yanzu akwai matsala a kafarsa ta dama sakamakon tsagewar kashi da ya samu," Real Madrid ta fada a wani sako da ta wallafa.

Ta kara da cewa: "Za a ci gaba da ba shi kulawar da ta kamata."

Duk da cewa ba a bayyana tsawon lokacin da zai yi jinyar ba, ana ganin Zinedine Zidane zai je filin wasa na Camp Nou ba tare da dan kasar Belgium din ba a ranar 18 ga watan Disamba, saboda girman raunin.

Wasannin Real Madrid na gaba:

  • 7 Disamba Real Madrid - Espanyol (LaLiga)
  • 11 Disamba Club Brugge - Real Madrid (Champions League)
  • 15 Disamba Valencia - Real Madrid (LaLiga)
  • 18 Disamba Barcelona - Real Madrid (LaLiga)

Kungiyoyin biyu dai su ne a saman teburin La Liga kowaccensu da maki 31.

Teburin La Liga