Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jose Mourinho: Kocin Tottenham ya ce an rufe babin Man Utd
Jose Mourinho ya ce lokacinsa a Manchester United ya riga ya wuce, yayin da ya shirya jagorantar Tottenham zuwa Old Trafford don fafatawa a ranar Laraba.
Mourinho ya bar United a watan Disambar 2018 bayan ya dauki shekara biyu da rabi a matsayin kocin kungiyar.
Dan kasar Portugal din bai sake jagorantar wata kungiya ba har sai a watan jiya da ya karbi jagorancin Tottenham, inda ya samu nasara a wasanninsa uku.
"Wannan maganar an riga an rufe ta. Na riga na bar kulo din, na dauki lokaci ina juya abubuwan da suka faru a baya," in ji Mourinho.
"Na kuma dauki lokaci ina shiryawa kaina irin kalubalen da zan fuskanta a nan gaba.
"Gaskiya, United a wurina tana cikin kundin bayanan yadda na gudanar da ayyukana, wato tana cikin littafin tarihi da na adana."
Mourinho ya bar United lokacin tana mataki na shida a saman teburin Premier. Yanzu haka tana mataki na tara karkashin jagorancin Ole Gunnar Solskjaer, maki biyu ne tazara tsakaninta da Tottenham, wadda ke na biyar a saman teburi.
Kocin, mai shekara 56, ya lashe gasar Lig, Europa da kuma kofin kalubale a lokacin yana United.
Mourinho ya ce: "Nan gaba zan ziyarci kungiyar a matsayin tsohon kocinta domin samun galaba a kanta."
"Ina fatan a wasan da za mu yi da su hakan zai sanya su manta da ni."