Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier League: Chelsea ta zama ta biyu a teburi
Tawagar Frank Lampard ta zama ta biyu a saman teburin Premier bayan ta lallasa Crystal Place da ci 2-0 a filin wasa na Stamford Bridge.
Dawowar dan wasa Ngolo Kante ya taimaka wa tsakiyar Chelsea sosai, ganin yadda da ma aka dakatar da Jorginho daga taka-leda.
Wannan shi ne wasa na shida da Chelsea ta ci a jere, abin da ya ba ta damar darewa mataki na biyu a teburi da maki 26 cikin wasa 12.
Tammy Abraham dan kasar Ingila ne ya bude wasan da kwallonsa ta farko, wadda ya ci bayan Willian ya ba shi ita a cikin yadi na 18 din Crystal Palace.
Kazalika, Abraham ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci wa Chelsea kwallo sama da 10 a Premier- shekarunsa 22.
Sai a minti na 79 ne Christian Pulisic dan kasar Amurka ya jefa ta biyu - Zouma ne ya hango shi a cikin yadi na 18 din Palace, inda shi kuma ya goga mata kai kuma ta gangare zuwa cikin raga ba tare da mai tsaron Guita ya iya yin komai ba.