An kaddamar da alamar kofin duniya

The official 2022 FIFA World Cup Qatar logo flashes on an electronic billboard at Times Square

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Qatar ta doke kasashen Amurka da Australia da Koriya ta Kudu da Japan wurin karbar bakuncin gasar a 2022

An kaddamar da alamar gasar cin kofin duniya ta 2022 a wasu birane 27 a fadin duniya, wanda Qatar za ta karbi bakunci.

Cibiyar Al'adu ta Larabawa ce ta tsara shi, wanda aka yi a jikin wani kyalle mai dauke da bayanin cewar a lokacin hunturu za a yi gasar, karon farko da za a yi a wannan yanayin.

An saka irin wannan kyallen mai dauke da zaren gasar kofin duniya a dandalin Leicester da ke birnin Landan, da na Time da ke birnin New York na Amurka, da Gare du Nord a kasar Faransa.

Za a fara gasar cin kofin duniya ranar 21 ga watan Nuwambar, a kuma yi wasan karshe ranar 18 ga watan Disamba, daidai da ranar samun 'yancin kan kasar ta Qatar.

A Shekarar 2010 ne Qatar ta yi nasarar samun gurbin karbar bakuncin kofin duniya da za ta gudanar a 2020, bayan da ta lashe da yawan kuri'a da aka kada.

Ta kuma yi nasara ne kan kasashen da suka yi zawarci tare da suka hada da Amurka da Australia, da Koriya ta Kudu da kuma Japan.

An yaye zanen a tsohuwar kasuwar Waqif da ke birnin Doha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kafa katon allon zanen a gine-gine masu muhimanci a Qatar
Birnin Buenos Aires na Faransa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A birnin Buenos Aires na kasar Argentina kuwa, an kafa allon da ke aiki da wutar lantarki wanda ke nuna zanen cikin launi daban-daban