Koscielny ya bar Arsenal, Rooney zai karbi Derby County

Laurent Koscielny

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal ta sayar da dan wasan bayanta Laurent Koscielny ga kungiyar Bordeaux a kan fan miliyan 4.6.

Shi ma tsohon dan wasan Ingila Wayne Rooney zai koma kulob din Derby County a matsayin dan wasa kuma koci daga watan Janairu.

Kungiyar Everton ta tanadi fan miliyan 100 don sayan dan wasan Crystal Palace, Wilfried Zaha, mai shekara 26, inda za ta bayar da 'yan wasa biyu Cenk Tosun na Turkiyya da kuma James McCarthy na Ireland, in ji jaridar Sun.

Ana sa ran dan wasan Ivory Coast Wilfred Zaha zai koma Everton zuwa karshen kasuwar saye da musayar 'yan wasan Turai kuma Palace za ta karbi tayin fan miliyan 65, in ji jaridar Independent.

Wilfried Zaha

Asalin hoton, Getty Images

Juventus ta shirya mika wa Manchester United 'yan wasa uku don karbar Paul Pogba mai shekara 26, a cewar Mirror.

Manchester United ta shirya sayen dan wasan Tottenham, Christian Eriksen, bayan dan wasan Sporting Lisbon da Portugal Bruno Fernandes wanda United din take nema ya zabi koma wa Tottenham, a cewar AS.

Leicester City ba za ta sayi dan wasan Bournemouth Nathan Ake a bana ba, an taya dan wasan a kan fan miliyan 75, in ji Sky Sports.