Messi na cikin 'yan takarar gwarzon Fifa na bana

'Yan kwallon Liverpool, Virgil Van Dijk da Mohamed Salah da kuma Sadio Mane suna daga cikin 'yan wasa 10 da za a fitar da gwarzon dan kwallon kafa na bana.

Sauran sun hada da dan wasan Tottenham Harry Kane da tsohon dan kwallon Chelsea Eden Hazard wanda yanzu yana Real Madrid, sai Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da fitaccen dan wasan Paris St Germain Kylian Mbappe.

Sauran cikon goman sun hada da Frenkie De Jong na Ajax da Matthijs De Ligt, wanda ya koma Juventus.

Haka kuma kocin Liverpool Jurgen Klopp, da na Tottenham Mauricio Pochettino, wadanda suka kara a wasan karshe a Champions League suna cikin takarar wanda ya fi taka rawar gani.

Shi ma mai horas da Manchester City Pep Guardiola, wanda ya lashe kofi uku a Ingila har da na Premier yana cikin takarar kocin da babu kamarsa a bana.

Sauran da ke yin takara sun hada da kocin Algeria, Djamel Belmadi da na Faransa, Didier Deschamps.

Sai kuma mai horas da River Plate, Marcelo Gallardo da kocin Peru, Ricardo Gareca da na Portugal Fernando Santos da na Ajax Erik Ten Hag da na Brazil, Tite.

Za a fitar da zakaran bana ta hanyar zabe da masu kallon tamaula sau da kafa za su yi da 'yan jarida da masu horar da tawagar kwallon kafa ta kasa da kyaftin-kyaftin dinsu.

Za a yi bikin karrama gwarzon bana a birnin Milan ranar 23 ga watan Satumba.

Masu takarar Gwarzon dan kwallon kafa na duniya na bana

  • Virgil van Dijk, Netherlands
  • Sadio Mane, Senegal
  • Mohamed Salah, Egypt
  • Harry Kane, England
  • Cristiano Ronaldo, Portugal
  • Lionel Messi, Argentina
  • Matthijs de Ligt, Netherlands
  • Frenkie de Jong, Netherlands
  • Kylian Mbappe, France
  • Eden Hazard, Belgium

Masu takarar gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta duniya ta bana

  • Lucy Bronze, England
  • Julie Ertz, United States
  • Caroline Graham Hansen, Norway
  • Ada Hegerberg, Norway
  • Amandine Henry, France
  • Sam Kerr, Australia
  • Rose Lavelle, United States
  • Vivianne Miedema, Netherlands
  • Alex Morgan, United States
  • Megan Rapinoe, United States
  • Wendie Renard, France
  • Ellen White, England

Mace mai horaswa da babu kamarta a bana

  • Phil Neville, England
  • Jill Ellis, United States
  • Milena Bertolini, Italy
  • Peter Gerhardsson, Sweden
  • Futoshi Ikeda, Japan
  • Antonia Is, Spain
  • Joe Montemurro, Arsenal
  • Reynald Pedros, Lyon
  • Paul Riley, North Carolina Courage
  • Sarina Wiegman, Netherlands

Masu takarar kocin da yafi taka rawar gani a bana

  • Jurgen Klopp, Liverpool
  • Pep Guardiola, Manchester City
  • Mauricio Pochettino, Tottenham
  • Djamel Belmadi, Algeria
  • Didier Deschamps, France
  • Marcelo Gallardo, River Plate
  • Ricardo Gareca, Peru
  • Fernando Santos, Portugal
  • Erik Ten Hag, Ajax
  • Tite, Brazil