AFCON 2019: Banana Banana da Super Egos na cashe wa juna a Twitter

Asalin hoton, Getty Images
Sa'o'i kafin daya daga cikin manyan wasannin AFCON 2019, magoya bayan Najeriya da Afirka Ta Kudu suka take nasu wasan a shafukan sada zumunta.
Dama can kasashen biyu suna gogayya da juna, inda kowacce take jin cewa ita ce uwa a Afirka, kuma saboda muna a shekarar 2019 ne hamayyar ta kara samun tagomashi a soshiyal midiya.
Tuni 'yan Najeriya suka fara kuri a Twitter tare da canza wa kungiyar Bafana Bafana suna zuwa "Banana Banana", su kuma 'yan Afirka Ta Kudu suka kira su da "Super Ego".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Sai dai Su ma 'yan Afirka Ta Kudu ba a bar su a baya ba. Wannan cewa yake 'yan Najeriyar nan "sai hayaniya suke kamar yadda suka saba yi a fina-finansu:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Wani kuwa tuna wa 'yan Najeriyar ya yi cewa su ne fa suka fatattaki masu masaukin baki:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Najeriya dai ta doke mai rike da kambun Kamaru ne kafin ta kawo wannan matakin, ita kuma Afirka Ta Kudu mai masaukin baki wato Masar ta doke.
Tsautsayi dai ya hada kasashen biyu tun a wasannin cancantar shiga gasar ta bana, kuma Bafana Bafana ce ta lallasa Super Eagles ta ci 2-0 har gida, inda awasa na biyu kuma aka yi 1-1 a birnin Johannesburg.
Har wa yau, kasashen biyu sun gwabza a wasannin cancantar shiga gasar ta shekarar 2015 wadda Najeriya ba ta samu zuwa ba, inda suka yi kunnen doki a dukkanin wasannin guda biyu - 0-0 da 2-2.
Amma fa idan maganar karawa ake a wasannin karshe na gasar, to Supoer eagles ce kan gaba. Sun doke Bafana Bafana har sau biyu a shekarun 2000 da kuma 2004.