Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta hau teburin Premier League
Manchester City ta koma ta daya kan teburin Premier League, bayan da ta doke Cardiff City 2-0 a wasan mako na 33 da suka kara a Etihad ranar Laraba.
Kevin de Bruyne ne ya ci kwallon farko minti shida da fara tamaula, sannan Leroy Sane ya kara na biyu daf da za a je hutun rabin lokaci.
Yadda kungiyoyin biyu suka murza leda
Da wannan sakamakon City ta hada maki 80 kenan, Liverpool ta koma ta biyu da maki 79.
City na fatan lashe kofi hudu a bana, bayan da ta fara daukar Caraboa, za ta buga wasan daf da karshe a FA Cup, za kuma ta fafata da Tottenham wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League.
Haka kuma kungiyar ta Etihad wadda ita ce lashe kofin Premier League na bara, yanzu tana ta daya da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool.
Sauran wasannin da suka rage na Man City:
Lahadi 14 Afirilu 2019
- Crystal Palace da Man City
Asabar 20 Afirilu 2019
- Man City da Tottenham
Laraba 24 Afirilu 2019
- Man Utd da Man City
Lahadi 28 Afirilu 2019
- Burnley da Man City
Asabar 4 Mayu 2019
- Man City da Leicester
Sunday 12 Mayu 2019
- Brighton da Man City