Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman ya musanta shirin sayen Man Utd

Saudi Arabia Crown Prince Mohammed Bin Salman

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Oktoba aka soma watsa rahoton cewa Yarima Mohammed Bin Salman na shirin sayen United.

Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed Bin Salman ya musanta rahotannin da ke alakanta shi da son sayen kulob din kwallon kafar Manchester United a kan £3.8bn.

A karshen makon jiya ne aka rika watsa jitar-jitar, ko da yake masu United, iyalan Glazers basu ce suna son sayar da kulob din ba.

A watan Mayun 2005 ne Amurkawan suka sayi kulob din a kan £790m.

Sai dai Turki al-Shabanah, mai magana da yawun Yarima Mohammed Bin Salman, ya ce "Rahotannin da ke alakanta Yarima Mohammed Bin Salman da shirin sayen Manchester United ba gaskiya ba ne."

"Manchester United ta gudanar da taro da Asusun tsimi da tanaji kan samun damar daukar nauyi. Amma ba a cimma matsaya ba."