Real Madrid ta musanta cimma yarjejeniya da PSG kan Mbappe

Real Madrid ta musanta rahotannin da suka ce ta cimma yarjejeniya tsakaninta da Paris St-Germain kan Kylian Mbappe.

A ranar Laraba ne wasu rahotanni suka ce Real Madrid da PSG sun cimma yarjejeniya kan matashin dan wasan na Faransa.

Real Madrid ta musanta rahotannin a cikin wata sanarwar da ta fitar.

Karo na biyu ke nan a mako daya da Real Madrid ta yi watsi da rahotannin da ke cewa tana dab da karbo Neymar na Brazil daga PSG.

A shafin Twitter ne wani dan jaridar Faransa ya kwarmato cewa PSG ta amince Real Madrid ta biya kudi fam miliyan 240 a kan Mbappe mai shekara 19.

Amma a cikin sanarwar da ta fitar, Real Madrid ta ce "labarin karya ne."

A watan Agustan bara ne PSG ta karbo aron Mbappe daga Monaco da nufin mallakar dan wasan kan kudi fam miliyan 166 a ranar 1 ga watan Yuli.

Mbappe na cikin tawagar Faransa da ke buga gasar cin kofin duniya, inda kawo yanzu ya ci kwallaye uku a gasar.