Koriya ta cire Jamus daga Russia 2018

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Kasar Koriya ta Kudu ta cire Jamus daga gasar Cin Kofin Duniya wadda ake ci gaba da yi a kasar Rasha, bayan ta doke ta da ci 2-0.
Koriya ta jefa kwallon farko ne a minti 92 - ta hannun Kim Young-gwon, sai kwallon da Son Heung-min ya ci a cikin minti na shida da aka kara kafin kammala wasan.
Kasar Jamus ce take rike da kofin bayan ta lashe gasar da aka yi a kasar Brazil a shekarar 2014.
A rukunin F, kasashen Sweden da Mexico ne suka tsallake zuwa gayayen gaba na gasar, yayin da Koriya ta Kudu da Jamus suka fita daga gasar.
Rabon da a fitar da Jamus daga gasar a matakin rukuni tun a shekarar 1938, kuma sau hudu kasar ta lashe gasar a tarihi.

Asalin hoton, Getty Images
Karanta wadansu karin labarai







