Lionel Messi ya yi wasa 300 a Camp Nou

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Lahadi Barcelona ta buga canjaras tsakaninta da Getafe a gasar cin kofin La Liga a wasan mako na 23.
Lionel Messi ya buga karawar wadda ita ce ta 300 a manyan wasanni da ya taka-leda a filin Camp Nou.
Cikin wasa 300 da ya yi a filin ya ci kwallo 212 a fafatawa 201 a gasar La Liga, ya kuma buga wasa 56 a gasar cin kofin Zakarun Turai nan kuma ya ci kwallo 55.
Dan wasan na tawagar kwallon kafa ta Argentina ya yi wasa 34 ya ci kwallo 31 a gasar Copa del Rey, sannan cikon tara ya buga Super Cup ya ci kwallo 11 a dai filin na Camp Nou.
Kungiyar da Messi yafi ci a filin Camp Nou ita ce Sevilla wadda ya zura wa kwallo 19, sai Espanyol 19, sannan Valencia da Osasuna da Athletic wadanda ya ci kwallo 16 kowacce.







