Harry Kane zai maye gurbin Benzema a Madrid

Kungiyar Real Madrid ta zabi dan wasan Tottenham, Harry Kane a matsayin wanda zai iya maye gurbin Karim Benzema a Santiago Bernebeu in ji jaridar Diario Gol da Daily Mirror.

Ita kuwa jaridar The Sun ta ce Daraktocin Manchester United na fargabar Jose Mourinho ya shirya barin kungiyar a karshen kakar bana, kuma Paris St-Germain zai koma da horar da tamaula.

Ita kuwa Daily Mirror cewa ta yi kocin na Manchester United, Jose Mourinho zai sayi dan kwallo a Janairu, kuma Samuel Umtiti na Barcelona ke son yin zawarci.

Neymar na yin iya kokarinsa domin ya shawo kan Philippe Countinho na Liverpool ya koma Paris St-Germain da taka-leda in ji Le 10 Sports da Daily Mirror.

Daily Mirror ta kuma wallafa cewar Sergio Aguero ya ce zai bar Manchester City a karshen kakar 2019, zai kuma koma kungiyar da ya fara buga kwallon kafa wato Independiente ta Buenos Aires din Argentina.