Yadda yankin Katari zuwa Rijana ya gagari jami'an tsaron Najeriya

Fasinjoji na rububbin bin jirgin kasa saboda kaucewa hare-haren 'yan bindiga a hanayar Abuja zuwa Kaduna

Asalin hoton, NRC

Bayanan hoto, Fasinjoji na rububbin bin jirgin kasa saboda kaucewa hare-haren 'yan bindiga a hanayar Abuja zuwa Kaduna
    • Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Matsalar tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna na sake zama babbar barazana musamman a wannan lokaci da hanyar da galibin mutane suka runguma na bin jirgin kasa domin neman tsira ke fuskantar wata sabuwar barazanar.

Harin da 'yan bindiga suka kai ranar Litinin da daddare tare da garkuwa da jama'a da dama a jirgin kasa da ke hanyar Kaduna daga Abuja ya sake jefa tsoro a zukatan matafiya.

Galibin 'yan kasar na cewa kusan babu zaɓin da ya rage garesu ganin cewa hanyar mota ba tsaro ga na jirgin kasa ma na fuskantar hare-haren 'yan bindiga.

Garuruwan Katari zuwa Rijana sun kasance yankin da 'yan bindiga ke yawaita cin karensu babu babbaka kan matafiya, inda ko a wannan lokaci ana suka tare jirgin kasa tare da buɗewa fasinjoji wuta.

Mutane da ake cewa sun rasu sun kai bakwai sannan sama da 22 sun jikkata, akwai kuma da dama da ba a ji duriyarsu ba tun bayan hari kan jirgin da ke dauke da fasinjoji 970.

Harin ya zo ne kwana guda bayan harin da 'yan bindiga suka kai tashar jirgin sama da ke Kaduna.

Wannan yanayi ya dimauta 'yan Najeriya da dama musamman ganin yadda matsalar tsaro ke neman hana su zirga-zirga da bin hanyar da kasance wajibi ga duk mutumin da ke son zuwa yankunan Arewa maso yamma da Arewa maso gabashin kasar daga Abuja.

Masana dai na ganin matsalar tsaro a Najeriya na ci gaba da gaggara hukumomi ganin cewa a kodayaushe da an soma tunanin sauki sai abubuwa su sake rincabewa.

A ina aka gaza?

Dr. Kabiru Adamu wanda ke nazari da sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya na cewa da alama yanayin da ake ciki yankin Katari zuwa Rijana na neman gagarar jami'an tsaro.

A tattaunwarsa da BBC ya ce ba abin makami ba ne a ce akwai manufar siyasar kan abubuwan da ke faruwa kan tsaro a Najeriya, sai dai ya ce wannan batu zargi ne.

Ya kuma ce kusan abin da kowa ke ɗiga ayar tambaya kenan a kai, kuma dama idan irin wadannan abubuwa na faruwa ba a daukan matakan da suka dace dole ba za a ga wani sauki ko sauyi ba.

Masanin ya ce akwai bukatar yin bincike mai zurfi domin gano ainihin matsalar abubuwan da ke faruwa a wannan yanki na Kaduna da kuma dalilin ya sa ya kasance matattara 'yan bindiga.

Ya nuna takaicinsa kan abubuwan da ke faruwa, sannan ya ce babu shakka akwai kura-kurai da dole sai an gyara domin ganin wani ci gaba.

Sannan ya ce akwai yankunan da ya kamata ace an dakile da daukan matakai da ake ganin akwai sake.

Ya kuma ce layin-dogo na jirgi akwai matakan da ya kamata a ce ana dauka wanda batun gaskiya ba a daukan wajen karesu da fasinjoji matafiya.

Ya ce akwai matakai na inganta tsarin tsaro da tattara bayanan sirri wanda kwata-kwata babu tsari, shi yasa hanyar titi da layin-dogo duk ake cikin barazana.

Dr. Kabiru ya kuma tabo batun rauni a fanin tsaron kasar sosai, wanda ya ce dole sai an tashi tsaye domin iya gyarawa ko ganin wani sauyi.

Hare-haren baya

Yadda 'yan bindiga suka lalata wani jirgin kasa a hare-harensu na baya a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Asalin hoton, NRC

Bayanan hoto, Yadda 'yan bindiga suka lalata wani jirgin kasa a hare-harensu na baya a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Ko a watan Oktoban 2021 dai da aka dakatar da zirga-zirgar jiragen bayan wasu hare-hare da aka kai wa jirgin har sau biyu a jere.

An kai hare-haren a wancan lokaci shi ma tsakanin Rijana da Dutse, kuma harin ya jawo lalacewar layin dogon da jirgin ke bi.

A baya can ma an sha jifan jirgin inda gilasansa suka fashe ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, kamar yadda fasinjoji masu yawan bin jirgin da dama suka shaida mana.

Sannan kuma ko batun lalacewar jirgin ma an saba samun rahotanni a kai, don kuwa ya sha lalacewa a hanyar a wasu lokutan har sai an kawo wani kan ya ja wanda ya tsaya ɗin.