Yadda barayi suka kashe sufurin jiragen kasa a Afirka Ta Kudu

Disused railway station
Bayanan hoto, Yadda ciyawa da ta mamaye layukan dogo a kusa da tashar jirgin kasa ta Dunswart
    • Marubuci, Daga Vumani Mkhize
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Business, Johannesburg & Cape Town

Tashar jirgin kasa ta Dunswart ta kusa lalacewa baki dayanta.

A cikin ginin tashar, akwai wayoyin lantarki da ke lilo daga rufin ginin bayan da wasu bata-gari suka sace rufin ginin, kuma akwai ciyawa mai tsawo da ta mamaye layukan dogon wadda alama ce ta yadda hukumomi suka yi watsi da wannan muhimmin wurin.

Sai dai ba dadewar lokaci ne ya janyo lalacewar da wannan tashar da ke gabashin birnin Johannesburg ta yi ba, wanda birni ne da ya zama cibiyar kasuwancin Afirka ta Kudu.

Barayi ne da bata-gari suka ziyarci wurin.

Shekaru biyu da suka gabata tashar kalau take, amma yanzu idan ka leka wurin za ka ga ma'aikata da matafiya a gaban tashar na shiga motocin haya zuwa cikin birnin Johannesburg duk da tsadar da hawa motocin take da ita.

Lalacewar tashar jirgin kasa ta Dunswart alama ce ta koma-bayan da bangaren sufurin jiragen kasa na Afirka ta Kudu ke fuskanta.

Sign saying woman's toilet
Bayanan hoto, Cikin shekara biyu barayi sun lalata tashar jirgin kasa ta Dunswart

Afirka ta Kudu na da layukan dogo masu tsawon kilomita 30,000 wanda ya sa kasar ke kan gaba tsakanin dukkan kasashen nahiyar a bangaren sufuri, sai dai barayi sun sace kayayyaki masu yawa a kokarin da suke yi na samun kudade bayan sun sayar da karafen.

Hukumar Passenger Rail Agency of South Africa (Prasa), wadda ke kula da sufurin jirgin kasa ta soki yadda aka rika bayar da kwangilolin samar da tsaro a tashoshi da layukan jirgin kasa na Afirka ta Kudu.

Wannan matakin ne ya sa ta soke kwangilar, abin da ya taimaka wa barayi yi wa tashoshin tatas saboda babu masu gadinsu.

Ministan Sufuri Fikile Mbalula ne ke kula da bangaren sufurin jiragen kasa a hukumance, kuma ya sha suka saboda rikon-sakainar-kashin da ya yi wa batun samar da tsaro a tashoshin.

Yayin da yake jawabi a wani bikin kaddamar da taragun jirgin kasa da aka yi wa kwaskwarima, wanda aka yi a birnin Cape Town, Mista Mbalula ya yi alkawarin daukar tsauraran matakai domin kare kayan sufurin masu matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasar.

"Muna da wani tsarin samar da tsaro mai inganci da ya hada da jami'an tsaro da ma'aikatan samar da tsaro na Prasa. A cikin tsarin za a yi amfani da fasahar zamani ta yadda idan aka sace wayar lantarki, za mu aika da jam'ai dauke da makamai cikin kankanin lokaci," in ji shi.

Remains of a building and railway track
Bayanan hoto, Matsalar sace-sacen kayan sufurin jirgin kasa na da mummunan tasiri ga tattalin arzikin Afirka ta Kudu

Wannan matsalar ba ta tsaya kan wahalhalun da fasinjoji ke sha akan hanyarsu ta zuwa aiki da komawa gida ba ne kawai.

Tana da tasiri mai yawa ga tattalin arzikin kasar ta Afirka ta Kudu.

Talakawan kasar ne suka fi jin jikin wannan koma-bayan.

A kasa irin wannan da ke fama da rashin ayyukan yi ga 'yan kasar masu yawa, da karuwar matalauta, karancin jiragen kasa zai kara girman wagegen gibin da ke tsakanin 'yan kasar ta Afirka ta Kudu.