Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa ake samun matar auren da ke kashe kanta duk minti 25 a Indiya
- Marubuci, Daga Geeta Pandey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
Me ya sa dubban matan aure a Indiya suke kashe kansu duk shekara?
Wasu alƙalumman gwamnati sun bayyana cewa matan aure 22,372 suka kashe kansu a bara - wanda ke nuna matan aure 61 suka yi kisan kai a rana ɗaya ko kuma matar aure ɗaya duk bayan minti 25.
Kisan kan matan aure ya kai kashi 14.6 na yawan kisan kai 153,052 a Indiya a 2020 da sama da kashi 50 na jimillar matan da suka kashe kansu.
Haka ma abin yake a bara. Tun 1997 lokacin da hukumar tattara alƙaluma ta NCRB ta fara tattara alƙalummanta kan kisan kai kan ɓangaren ayyukan yi, sama da matan aure 20,000 ken kashe kansu duk shekara. A 2009, adadin ya ƙaruwa zuwa 25,092.
Rahotanni a ko da yaushe na ɗora laifin musababbin kashe-kashen da "rikicin gida" ko "rikicin da ya shafi aure." Amma me ya sa dubban mata ke kashe kansu?
Ƙwararre kan lafiyar ƙwaƙwalwa ya ce babban musababbi shi ne rikicin cikin gida - kamar yadda kashi 30 na mata suka bayyana wa wani binciken gwamnati da ya mayar da hankali kan matsalar rikicin aure - da kuma matsalolin da ke haifar da rikici a a gidajen aure.
"Mata suna da juriya da gaske, amma juriyar na da iyaka," in ji Dr Usha Verma Srivastava, masanin ilimin halayyar dan adam da ke arewacin birnin Varanasi.
"Yawancin yara ana aurar da su da zarar sun kai shekara 18 - shekarun da aka ƙayyade na aure. Ta zama matar aure kuma suruka inda za ta shafe yini a gida, tana girki da shara da goge da ayyukan gida. Duk wasu sharuɗɗa an shata mata, ba ta da wani ƴanci nata kuma ba ta da damar riƙe kuɗi nata."
"Iliminta da burinta ba ya da wani amfani kuma a hankali zai dusashe, rashin jin daɗi da yanke ƙauna za su bijiro kuma ci gaba da rayuwa a haka zai zama kamar wata azabtarwa.
Ga manyan mata, a cewar Dr Verma Srivastava, dalilin kisan kai ya bambanta.
"Da yawansu suna fama da rashin lafiyar kaɗaici bayan yara sun girma sun bar gida wasu kuma yawanci sun fara fuskantar alamomi na manyantakar mace wanda zai iya haifar da damuwa da shiga yanayi na baƙin ciki."
Amma kisan kai, a cewarta, ana iya magancewa "idan aka yi ƙoƙarin hana mutum cikin dakiƙa, akwai yiyuwar za su tsaya."
Wannan saboda, kamar yadda likitan taɓin hankali Soumitra Pathare ya bayyana, yawancin kisan kai na Indiyawa na faruwa ne cikin rashin hankali. "Namiji ya dawo gida, ya lakaɗa wa matarsa duka, ita kuma sai ta kashe kanta."
A cewarsa wani bincike mai zaman kansa, ya nuna kashi ɗaya bisa uku na matan Indiya da ke kashe kansu suna da tarihin da ya shafi rikici na cikin gida. Amma kuma wannan ba ya cikin dalilin da rahoton NCRB ya bayyana.
Chaitali Sinha, likitar masu lalurar ƙwaƙwalwa, ta ce "mata da yawa da ke fama da rikicin cikin gida suna yin shiru ne domin sun san ba wani taimako da za su samu."
Ms Sinha, wacce ta yi aiki tun da farko a asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa a Mumbai, tana bayar da shawarwari da kula ga waɗanda suka yi yunƙuri halaka kansu, ta ce ta gano cewa mata sun samar da wa kansu wani taimako a lokacin da suke balaguro a jirgin ƙasa ko tare da ƴan uwansu.
"Ba su da wata hanya ta bayyana matsalolinsu wani lokaci ta wannan lokacin balaguron suke samun damar tattaunawa da wani lokaci mutum ɗaya," in ji ta, tana mai cewa kullen korona ya ƙara tsananta matsalolinsu.
"Matan aure sukan samu sa'ida idan mazajensu sun fita aiki, saɓanin lokacin kullen korona, inda rikicin cikin gida ya tsananta saboda matan sun faɗa tarkon masu cin zarafinsu.
"Wannan ya ƙara takaita walwalarsu da kuma ikon da suke da shi na yin wasu abubuwa da suke samun farin ciki. Don haka bakin ciki na ƙaruwa daga nan tunanin kisan kai sai ya bijiro.
Indiya ce ta fi bayar da rahoton yawan masu kashe kansu a duniya: Mazan Indiya sun kai kashi ɗaya bisa hudu na yawan masu kashe kansu a duniya, yayin da matan ƙasar suka kai kashi 36 na yawan masu kashe kansu a duniya a tsakanin ƴan shekara 15 zuwa 39.
Sai dai Dr Pathare wanda ya yi bincike kan hana kisan kai, ya ce alƙalumman na Indiya sun zarta haka ba su fayyace girman matsalar ba.
"Idan ka yi nazari kan binciken mutuwar mutum miliyan ɗaya (wanda ya mayar da hankali kan mutum miliyan 14 a gidaje miliyan 2.4 tsakanin 1998 zuwa 2014) ko kuma binciken mujallar Lancet, ba a bayar da cikakken rahoto kan yawan kisan kai a Indiya ba da kusan tsakanin kashi 30 zuwa 100.
Kisan kai, a cewarsa, "ba a yin maganarsa a tsakanin al'umma - akwai kyara da ke tattare da shi, kuma yawancin gidaje suna ɓoye wa. A yankunan karkara na Indiya babu hanyoyi na yin bincike kuma masu hannu da shuni na fakewa da ƴan sanda da ke ɓoye kisan kai su ce hatsari ne. Kuma ba a tabbatar da sahihancin bayanan da ƴan sanda ke ɗauka ko alƙalummansu."
A lokacin da Indiya samar da wani shirin hana kisan kai, Dr Pathare ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne a samu ingancin alƙalumma.
"Idan ka dibi yawan yunkurin da wasu suka yi na kashe kansu a Indiya, babu yawa. Ko ina a duniya, sun sun kai sau huɗu zuwa 20 na yawan asalin yawan kisan kai. Don haka idan Indiya ta ce mutum 150,000 suka kashe kansu a bara, yunƙurin kisan kai zai kai tsakanin 600,000 zuwa miliyan shida.
"Majalisar Ɗinkin Duniya burinta shi ne ta rage yawan kisan kai da kashi ɗaya bisa uku zuwa 2030, amma a shekarun baya, namu ya ƙaru da kashi 10 idan aka kwatanta da shekarun baya. Kuma rage shi wani buri ne da ba ya da tabbas."