Shirin makamin nukiliyar Iran: Barazanar hare-haren Isra'ila na karuwa

Jirgin yakin Isra'ila samfurin F-16 a sansaninta da ke Ovda, kusa da kudancin birnin Eilat, a lokacin atisayen Blue Flag a ranar 24 Oktoba shekarar 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A baya-bayan nan Isra'ila na atisayen sojoji da aminanta
    • Marubuci, Daga Yolande Knell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem

A karon farko sojin ruwa na kasashen Isra'ila da Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa sun fara atisayen hadin gwiwa na tabbatar da tsaro ta hanyar amfani da jirgin yakin ruwa na Amurka.

Wannan ya biyo bayan tashin hankalin da aka samu a sansanin sojin sama da ke arewacin birnin Eilat mai tashar ruwa a Isra'ila, da hadin gwiwar jiragen yakin kasar da wasu kasashen.

Irin wannan atisaye dai na tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro, ma'ana gargadi ake yi wa Iran a fakaice, wadda a baya-bayan nan take gudanar da gagarumin atisayen soji da sauya dabarun gudanar da ayyukanta.

Sai dai hakan na zuwa ne daidai lokacin da Isra'ilawa ke nuna damuwa kan ko kasar na gab da fadawa barazanar hare-haren nukiliyar Iran.

Gwamnati ta ware dala biliyan daya da miliyan dari biyar domin shirin ko-ta-kwana ga sojojin Isra'ila domin kai hari cibiyar makami mai linzamin Iran. Haka kuma kusan kowacce rana 'yan siyasa da shugabannin soji na gargadi kan yiwuwar kai wadannan hare-hare.

1px transparent line

Ina ta kokarin jin ta bakin manyan masu sanya ido kan shirin Iran na kerama makamin nukiliya da masu sharhi kan al'amura kan abin da suke ganin zai faru nan gaba.

Wani jami'an tsaro a Isra'ila ya shaida min cewa:"Isra'ila ba ta da aniyar yaki da Iran, amma ba za mu nade hannu mu zuba ido Iran ta mallaki makaman nukiliya ba. Idan mukai duba ga shirin ta na fadada makaman nukiliya, zan iya cewa mun shirya tsaf domin samawa kanmu mafiutar da ta dace."

Wannan na zuwa ne bayan tattaunawa tsakanin Iran da manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, a fakaice har da Amurka a shekarar 2015, kan yarjejeniyar da aka kira ta hadin gwiwa na dakatar da Iran daga abin da take yi da ya sabawa abin da aka cimma a baya da kuma ake sa ran za a ci gaba da wannan tattaunawa a ranar 29 ga watan Nuwamba a babban birnin Australia wato Vienna.

Yarjejeniyar ta JCPOA, na da aniyar ragewa da rufe cibiyar makamin nukiliyar Iran, inda kwararru za su kai ziyara domin gani da ido ko tana amfani da ita. Idan ba a manta ba a shekarra 2018 ne Amurka karkashin mulkin Shugaba Donald Trump ta fice daga yarjejeniyar da amincewar Isra'ila.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi (hagu) lokacin da ya ke magana a wajen cibiyar makamin nukiliya ta Bushehr da ke kasar (8 Octoba 2021)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Iran t dade ta na nanata shirin ta na makamin nukiliya ba na tashin hankali ba ne

A daidai lokacin da ake shirin komawa teburin tattaunawa kan batun, Iran ta sanar da samar da kilo giram 25 na makamashin uranium, wato kashi 60 kenan cikin 100 na abin da ake bukata wajen hada makamin nukiliya.

Yayin da Iran ta ci gaba da kafewa shirin kera makami mai linzaminta ba mai cutarwa ba ne, a bangare guda su kan su masu sharhi a kasar sun disa yar tambaya kan yawan sinadarin da ake amfani da shi a baya-bayan nan ka iya zama barazana nan gaba.

"'Yan Iran na gab da samar da kayan hada makamin nukiliya, fiye da wanda muka gani a baya," in ji wani jami'in tsaro a Isra'ila. "Wannan kadai ya isa zama barazanar tsaro ga Isra'ila."

Ma'aikatar tsaron Isra'il ta ce idan Iran ta ga dama cikin wata guda za ta iya kara inganta makamahin uranium din ta.

line

Danbarwar shirin makamin nukiliyar Iran: Muhimman abubuwa

  • Manyan kassahen duniya ba su amince da Iran: Wasu kasashen sun yi amanna da cewa Iran na son mallakar makaman nukiliya masu karfi, saboda ta na son kera ba din da aka hada daga makamin nukiliya, sai dai ta musanta hakan.
  • Dan haka sai aka cimma yarjejeniya: A shekarar 2015, Iran da kasashe shida masu karfin tattalin arziki na duniya suka cimma wata yarjejeniya. Iran za ta dakatar da kera makaman nukiliyar, ita kuma sai a saka ma ta da dauke takunkumin tattalin arzikin da ke kan ta.
  • Me cece matsalar a halin yanzu? Iran ta koma aikin kera makamin da aka haramta ma ta yi a baya, bayan shugaba Donald Trump ya janye Amirka daga yarjejeniyar, tare da kakabawa Iran takunkumi. Duk da cewa bayan nshugaba Joe Biden ya zama shugaban kasa ya nuna aniyar ske komwa, sai dai dukkan bangarorin biyu na ganin dan uwansa ne ya dace ya fara sanar da haka.
line

Lokaci na kurewa

Tsohon mai bayar da sha'awa kan shanin tsaro a Isra'ila, Yaakov Amidror, wanda a yanzu babban jami'i ne cibiyar tsaro da bincike ta Israla da ke birnin Kudus, ya dade da yin gargadi kan hatsrin da ke cikin aniyar Iran na kera makamin nukiliya tun a shekarun 1990, a lokacin da ya ke aiki a hukumar leken asiri.

Ya na da masaniya kan halin da ake ciki da wabda ya ke ganin za a fada nan gaba.

"Isra'ila ba za ta ci gaba da tafiya da abu irin haka ba, ta yadda Iran ke kara kusantar mallakar bama-bamai kare dangi, kuma dole nan ba da jimawa ba ta dauki matakin dakatar da hakan," in ji shi.

"Ban ga ta inda za a soma ba in dai ba ta hada bam ba domin ban ga alamar ja da baya ko karaya daga Iran ba na aniyarta wajen cimma mafarkin mallaka cibiyar makamin nukiliya mafi girma, sannan kawo yanzu mun ga yadda ta ke tafiyar da lamuranta."

Sau biyu Isra'ila ta na kokarin ganin bayan makiyanta nasu kera makamin nukiliya, wato Iraqi a shekarar 1981, sai kuma Siriya a shekarar 2007, sai dai hakan bai samu ba.

Sai dai yawancin masu sharhi na disa ayar tambaya kan ko Isra'ila ta na da karfin da za ta dakatar da aniyar Iran daga inganta makamin nukiliyar? Sannan idan hakan ta faru me zai biyo baya?

"Ko wa a Isra'ila ya haimci cewa kai wa Iran hari na nufin shiga yakin da ba asan inda zai tsaya ba," in ji Mista Amidror.

Iranta maida martani mai firgitarwa, inda ta ce ba za ta aminta da yi mata katsa landan a harkokin da suka shafi tsaron kasa ba, musamman ta fannin kai mata hari.

Za ta yi amfani da na ta jami'an tsaron da abokanta da ke yankin kamar Hezbolla a Labanun wadda ta mallaki dubun-dubatar makaman roka, da mayakan sa kai 'yan shi'a na Siriya da Iraqi, da 'yan tawayen Houthi a Yemen, da mayakan jihadi na zirin Gaza domin kariya daga Isra'ila da kawayenta.

Hezbollah members march in Baalbek, Lebanon (13/11/21)

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai duk da hadarin da ake gani a harkar, wasu a Isra'ila na da ra'ayin kai hare-haren ne kadai mafita, indai har hakan zai janyowa Iran koma bayan 'yan shekaru a fannin kera makamin nukiliyar.

A bangare guda kuma masu shiga tsakani na fatan ganin an samu sasantaw domin smun zaman lafiya a yankunan biyu.

"Ina fatan za ai nasara ta hanyar amfani da diflomaiyya, sai dai ba ni da tabbacin hakan," in ji Sima Shine, tsohuwar shugabar hukumar tsaro ta Mossad.

Gwamnatin shugaba Joe Biden na da aniyar maido da Iran teburin sulhu, duk da cewa gwamnatin Isra'ila ta nuna kin amincewa da hakan.

Matan Iran dauke da allon da aka rubuta aga karshen Amirka a lokacin zanga-zangar tunawa da shekara 42 mamayar ofishin diflomasiyyar Amirka a birnin Tehran

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Jami'an Iran sun ce shirin makamin nukiliyar abin alfahari ne ga 'yan kasar

Shekaru 10 da suka wuce, an samu rahotannin kai wa na'urori masu kwakwalwar Iran harin hadin gwiwa tsakanin Isra'ila da Amurka domin janyo nakasu ga shirinta na kera makamin nukiliya.

Ko a baya-bayan nan, Iran ta zargi Isra'ila da kisan kwararre kan hada makamin nukiliyarta, Mohsen Fakhrizadeh, wanda aka harbe a kusa da Tehran da taimakon wata bindiga samfurin mashinga, da kuma kai hari cibiyar makamin nukiliyarta da ya janyo lalacewar wasu kayayyaki, ko da yake daga bisani Iran ta ce babu abin da ya shafi kaya masu mhimmanci.

Wani bangare na cibiyar makamashi ta Natanz da ke Isfahan, a Iran (2 Juli 2020)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Iran ta ce abin da ya fashe a cibiyar makamin nukiya ta Natanz a watan Yuli 2020 wa makarkashiya ce da ba a yi nasara ba