Darasin 'yadda namiji zai kara aure' ya jawo ce-ce-ku-ce a Saudiyya

Lokacin karatu: Minti 3

Sanar da wani sabon darasin koya wa maza dubarun yadda za su ƙara aure ya haifar da ce-ce-ku-ce a Saudiyya, wanda har ya kai ga soke darasin baki ɗaya.

Wata ƙungiya ce ta Al-Bir ta shirya horar da maza a hedikwatarta da ke Ar-Rass na Saudiyya a darasin da aka yi wa taken "dubarun ƙara mace ta biyu."

Matakin ya gamu da fushin ƴan Saudiyya da sauran ƙasashen Larabawa inda suka dinga tsokaci a kafofin sadarwa na intanet.

Wani mai fafutika ya yaɗa hoton tallar darasin na shawarwarin ƙarin aure na ƙungiyar Al-Bir da ayyukanta suka shafi zamantakewa al'umma.

An dai samu ra'ayoyi masu cin karo da juna kan darasin amma yawancin na suka sun fi yawa, inda wasu ke ganin darussa na yadda za su samu ayyukan yi ne ko digiri na biyu da na uku ya kamata a koya masu amma sun yi mamakin ɓullo da wannan darasin a wannan lokacin.

Mafi yawanci tsokacin mutane na nuna ɓacin rai ne game da sanarwar.

Wasu ƴan Saudiyya na ganin ƙarin aure halal ne kuma yana da sharuɗɗa, abin da yake da muhimmanci shi ne idan mutum zai iya tabbatar da adalci kuma yana da arzikin kula da mata biyu. Don haka babu wani darasi da ake buƙata.

Wasu sun nuna cewa ba irin wannan darasin ake buƙata ba, kamar yadda @RUMAYH_SULAIMAN ya ce "ƙwarewar da matasan Rass suke buƙata shi ne na fannoni da dama na kasuwanci yanzu kuma ana masu maganar darasi kyauta kan dubarun ƙara mata.

Wasu da dama sun yi mamakin yadda ma aka amince aka yi amfani da tambarin burin Saudiyya na Vision 2030 a hoton tallar darasin.

Wasu sun bayyana darasin a matsayin wani babban abin takaici

A cewar @AzizAQ ya ce: "Wata ƙungiyar agaji kuma cibiyar ƙwararru za ta gudanar da kwas domin sanin dubarun ƙara mata. Wani babban abin takaici."

Wasu kuma na ganin darasin kamar " wata tsokana ce ga mata da cin zarafi da kuma nuna kaifin tunanin maza."

Faisal Al-Fraih ya ce kamata ya yi a ce "manufar darasin shi ne inganta dubarun zama da mace ɗaya, maimakon ƙara mata ta biyu."

Wasu kuma sun buƙaci a dakatar da ayyukan ƙungiyar tare da hukunta waɗanda ke da alhakin shirin.

Abin da waɗanda suka shirya darasin suka ce

Bayan ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara da sanarwar da haddasa, kungiyar da ta sanar soke darasin tare da bayar da umarnin goge tallar da aka yaɗa a kafofin sada zumunta na intanet.

A cikin wata sanarwa da jaridar Al Watan ta wallafa, Daraktan ƙungiyar Al-Bir da Ar-Ras Fahd Al-Sardah, ya ce kuskure ne aka samu daga wani sabon ma'aikaci kuma gaba ɗaya an soke tare da goge tallar da aka yaɗa a kafofin sadarwa na intanet.