Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hisbah: Ana ce-ce-ku-ce kan hotunan kwalliyar Zarah Bayero amaryar Yusuf Buhari
Hotunan yar Sarkin Bichi Zarah Nasiru Ado Bayero, wadda ɗan shugaban ƙasa Yusuf Buhari yake shirin aura, sun mamaye shafukan sada zumunta na intanet inda ƴan Najeriya ke ta ce-ce-ku-ce.
Gimbiyar ta gidan sarautar Kano da Yusuf Buhari zai aura a wannan wata na Agusta, bayanai sun ce hotunan da ake yaɗa wa nata sun fito ne daga wani bikin mata zalla da aka gudanar a Abuja a makon nan.
Ana ce-ce-ku-ce ne kan kwalliyar da Zarah Nasiru Ado Bayero ta yi ta farin tufafi da wasu ke ganin sun nuna tsaraicinta. Amma yawanci tsokacin ya fi karkata ne ga hukumar Hisbah ta jihar Kano da ke jaddada bin tsarin addinin Islama a jihar.
Sunan Hisbah ya kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a kafofin sada zumunta na intanet a Najeriya tun daga ranar Laraba zuwa Alhamis.
Duk da wasu na sukar hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta musamman saboda gidan da ta fito, wasu kuma na ganin hotunan ba su yi munin da har za a dinga ce-ce-ku-ce ba a bikin da aka yi na mata.
Irin wannan saɓanin ba wani sabon abu ba ne a arewacin Najeriya inda addinin Islama da al'ada suka fi yin yi tasiri sosai.
Me ake cewa?
Sanata Shehu Sani, tsohon ɗan majalisar dattawan Najeriya, yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi tsokaci kan hotunan na ƴar Sarkin Bichi inda ya soki malaman addini cewar: "Idan ƴaƴan talakawa suka yi wata shiga marar kyau wurin biki, malamai su dinga ihu, amma sai su yi gum idan ƴaƴan attajirai ne."
Sai dai @omogehrh ta mayarwa sanata Shehu Sani da martani inda ta ce "Ta yaya? A ina? Ni ban ga aibunta ba, kawai dai ta yi ƙanƙanta."
@jayB_10 ya soki hukumar Hisbah ne a Kano inda a tsokacinsa ya ce: Wannan ce da Yusuf Buhari zai aura. Ta yi shigar da ke nuna jikinta a bikin aure. Amma ba wannan ne labarin ba. Da bikin ƴaƴan talakawa ne da ta kai samame.
A nasa ra'ayin @lbn_Abdullah ya kare Hisbah ne inda ya ce idan gaskiya za a faɗa akwai waɗanda ya kamata a ɗora wa laifi, domin Hisbah tana da iyaka kuma ya kamata a yaba mata kan ƙoƙarin da ta ke.