Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Covid-19: Jarirai 200,000 da aka yi cikinsu a lokacin kullen korona a Philippines
- Marubuci, Daga Howard Johnson & Virma Simonette & Flora Drury
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Rovelie Zabala na dauke da tsohon cikin ɗanta na goma.
Yayin da muke wannan magana, matar mai shekara 41 na kishingide a cikin wani yanayi, tare da rungume ɗanta na tara.
''Carl, Jewel da Joyce….'' Kamar yadda Rovelie ke kiransa, Charlie mai shekaru shida ya yi wa mahaifiyarsa wani irin kallo na nuna rashin amincewa. ''Yi hakuri, sunansa Charlie,'' in ji Rovelie, cikin nuna rashin damuwa.
Sai bayan Rovelie ta haifi danta na bakwai ne sannan ta gane me ake nufi da tsarin iyali, amma na baya-bayan nan ba zato ta sake samun juna biyun, lokacin da aka tsaurara dokar kullen korona, wanda aka shaida yadda sojoji masu sintiri a kan titinan dauke da kayan yaki, shingayen binciken ababen hawa na hana kai-komo, kana mutum daya daga cikin kowane iyalai aka amince ya fita doimin sayen kayan abinci.
Kullen kuma na nufin cewa dubban mata ne suka kasa fita zuwa neman magungunan hana daukar ciki, da hakan ya haifar da samun juna biyun da ba a shirya ba kamar na Rovelie da aka samu a fadin kasar.
Ko shakka babu, an kiyasta karin samun haihuwar jarirai dubu dari biyu da goma sha hudu (214,000) a cikin shekara mai zuwa, kamar yadda cibiyar lura da yawan al'uma ta Jami'ar Philippines da hukumar kididdigar yawan jama'a da Mmajalisar Dinkin Duniya UNPF suka bayyana.
Wadannan yara za a haife su a asibitocin da suka makare da jarirai miliyan daya da dubu dari bakwai da ake haifa a duk shekara, kuma galibi daga iyalan da ke hannu baka hannu kwarya.
Kuma za a iya cewa soma taɓi ne. Saboda annobar ba ita kadai ba ce dalilin da ya sa ake kara samun haife-haifen a kasar ta Philippine.
Rovelie Zabala na dauke da tsohon cikin danta na goma.
Tumbin giwa
Manila babban birnin kasar ta Philippine, birni ne mai makare da al'umma, ana maganar mutane miliyan 13 a tsakanin yankin Manila Bay da tuddan Sierra Madre.
A takaice, mutane fiye da dubu 70 (70,000) ne a cunkushe a kowane murabba'in kilomita, kamar yadda bayanan yawan a'lumma na 2015 suka nuna.
Ana iya gane yawan a ko ina daga cunkoson ababan hawa zuwa gidajen yari, inda mutane ke kwance cunkushe kamar kifin gwangwani a daki daya da yawansu ya wuce kashi 30 bisa dari na yadda ya kamata ya dauki jama'a.
Kuma galibi matalauta ne suka fi zama a wurare masu cunkoson jama'a, inda wasu suka koma cin nama da aka zubar a bola.
Kwararru sun bayyana cewa galibi ana danganta talaucin kai tsaye ne da yawan haihuwa a kasar, yayin da bincike yan nuna haihuwar 'ya'ya biyu ga kowace mace guda, saboda yawan al'umma ya kasance bai zama fiye da kima ba, kuma bai yi kasa ba, ka iya bunkasa tattalin arzikin kasar wajen rage yawan 'ya'yan da ake haihuwa a cikin talauci.
Rage yawan haihuwar zai sa a samu cin gajiya mai yawa daga kasafin kudin kasar, tare da inganta rayuwar al'umma gabaki daya.
Gwamnatin kasar Philippine kuma ta san da hakan. Tun a shekara ta 1960 ta yi ta kokarin rage yawan haife-haife tare da samun nasarori.
Don haka, yayin da yawan jama'a ya kusa ninkawa sau uku daga miliyan 35 zuwa miliyan 110 a yanzu, adadin ya yi kasa daga kashi 6.4 a shekarar 1969 zuwa kashi 2.75 a shekarar 2020.
Duk da haka ba su kai rashin samu nasara kamar kasar Thailand a yankin Asia ba a lokaci iri daya.
Kasar mai bin addinin Budda ta rage yawan haihuwar kasa zuwa kashi 5.8 kan kowace uwa a karshen shekarar 1960 zuwa kashi 1.5 a shekarar 2020, kamar yadda kididdigar majalisar dinkin duniya ta nuna.
Kiyasin talaucinta yanzu ya kai kashi goma bisa dari idan aka kwatanta da na kasar ta Philippine mai kashi 17%.
Amma me yasa wannan banbanci? A wani bangaren, kasar Philippine na da Cocin Katolika mai fada ji, da ke tuhuma kan duk wanda ke adawa da amfani da magugunan hana daukar ciki, da kuma karfafa gwiwar a kara hayayyafa da ayoyin ''Ku zama masu adalci da kuma yaduwa.''
"Ko shakka babu za mu nuna adawa da hakan (daukar ciki),'' Fada Jerome Secillano, na babban taron Cocin Katolika na kasar ta Philippines ya shaida min a wata hira ta bidiyo.
Cibiyar haifar jarirai da yawa
Ma'aikaci a asibitin Dr Jose Fabella sun saba da zama cikin aiki a koda yaushe. A baya cikin shekarar 2012, asibitin na karbar haihuwa jarirai 120 a rana, da hakan ya sa aka yi wa dakin haihuwar lakabi da ''Cibiyar haifar jarirai da yawa''.
Abubuwa sun kara inganta, bayan da adadin ya ragu zuwa kusan rabi dun bayan da aka amince da shirin tsarin iyali na RHL a shekara ta 2012. Amma kuma yanzu suna kara shirya samun ''ƙaruwar yawan jarirai''.
Yayin da muka shiga dakin haihuwa na farko, mun ci karo da koke-koken jarirai babu ƙaƙƙautawa.
Dakin, wanda ya kai girman filin wasan kwallon kafa, na da jerin layukan gadajen karfe dai-dai da aka hade su.
Fankokin sun yi nesa da su, hakan ya sa wurin ya dumama da zafi. Masu jegon sun sha rigunan haihuwa, da takunkumin rufe fuska da garkuwar fuska, suna rike da jariransu.
"Yanzu haka, akwai akwai marasa lafiya uku ko hudu a kan gadaje biyu da aka hade wuri guda,'' Dr Diana Cajipe ta shaida mana.
"Abin takaici ba mu da isasshen fili, kuma duk da haka karin. wasu marasa lafiyar na nan zuwa. Zai iya kai wa mutane shida zuwa bakwai a kan gadaje biyu da aka hade.''
Kwayar cutar ba kawai tana haddasa matsalar yawan adadin ba kadai.
A watan da ya wuce dole sai da asibitin yu rufe na wucin gadi, bayan da wasu ma'aikatan jinya da masu taimaka musu bakwai suka kamu da cutar korona.
A irin wannan yanayi, babu wahalar gano yadda cutar ke yaduwa cikin sauri.
Hukumar gudanarwar asibitin na fatan ganin sabon ginin ya samar da karin filin saka gadaje, amma har yanzu babu komai a ciki.
Shugaba Duterte yana matukar goyon bayan tsarin iyali, in ji Mr Pernia, amma ''ya fi mayar da hankali kan muggan kwayoyi da cin hanci da rashawa'', inda yake sa kafar wando daya da masu tu'ammali da miyagun kwayoyin da masu safarar shi.
'Babban abin damuwa'
Rovelie ba ta san komai ba in ba talaucin da wadannan mazan ke magana a kai ba. Tana zaune ne a Baseco, Tondo, daya daga cikin yankuna masu cunkoson jama'a a yankin.
Amma kuma ta san da koyarwa da hudubar Cocin Katolika game da magungunan hana daukar ciki da kuma zubar da ciki.
"Lokacin da na samu ciki ya kai wata daya, na fada wa maigidana cewa ina son in zubar da shi saboda rayuwar akwai wahala,'' ta bayyana mana yayin da muka zaune kasa a bakin wani kogi, daya daga cikin wurare inda za ka samu kwanciyar hankali a wannan yanki.
"Amma ya ce ba damuwa za mu iya daurewa. Na kyale a maimakon in aikata zunubi.
''Ya kai kusan watanni uku da rabuwarmu.''
Yayin da ta ke goge hawaye, Rovelie ta ce damurwata it ace makomar 'ya'yanta.
Muna cikin haka mutane sun warwatsu bayan da wata motar jami'an 'yansanda da biyo da kan titin mai cike da trubaya tana farautar wani mai sayar da miyagun kwayoyi.
Sayar da miyagun kwayoyi, Rovelie ta nuna, daya daga cikin abubuwan ''tsira ne''.
Yanzu da yake annobar korona ta durkusar da tattalin arzikin Philippine, babu wata hanyar samun kudaden shiga kamar a da.
"Wannan shi ne babban abin damuwata, idan zan iya tallafawa karatunsu?'' in ji Rovelie.
"Wani lokaci idan haushi ya kama ni, na kan fusata, na kan fada musu, in da zai yiwu da na kai su riko gidan masu kudi don su samu ilimi mai inganci. Amma kuma sai in fada a raina cewa zan iya daurewa.''