Abin da ya sa dawowar farin ɗango ke barazana ga Gabashin Afirka

Turkana farmer Joseph Tirkwel asses the severe damage of his maize crops while hopper bands of Desert Locust ravage them in Napeikar, Turkana County, Kenya.

Asalin hoton, FAO/Luis Tato

Bayanan hoto, A kowace shekara sai fari sun gallabi yankin gabashin Afirka fiye da shekara 70 kenan yanzu
    • Marubuci, Daga Navin Singh Khadka
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan muhalli

Sabbin ayarin farin ɗango na yin barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a yankin Afirka da Yemen duk da shekara guda da aka kwashe ana gudanar da aikin daƙile su.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai kyakkyawan yanayin kiwo ga farin a gabashin Habasha da Somaliya, da kuma Kenya, wadda ita ma ke cikin haɗari.

Yanzu haka farin na ci gaba da yin ƙyanƙyasa a bangarori biyu na Bahar Maliya, abin da ke zaman wata sabuwar barazana ga Eritriya, da Saudiyya da Yemen.

Wannan shekarar dai ta riga ta ga kutse mafi girma da aka taɗa ganin cikin shekaru 70, kuma farin ɗangon ne suka yi shi.

Ta riga ta ga mamayewar Gabashin Afirka mafi munin cikin shekaru 70.

"Lamarin zai iya munana kamar yadda aka gani a shekarar da ta gabata "

Tsakanin watan Janairu da Agusta na wannan shekara Gabashin Afirka ya ga biliyoyin kwari masu lalata amfanin gona.

Gonjoba Guyo, wani makiyayi a yankin Arewacin da ke Kenya ya ce "Mun yi asarar yawancin wuraren kiwo da ciyayi saboda farin, haka har yanzu muna asarar dabbobinmu da yawa."

"Na rasa awaki 14, shanu hudu da rakuma biyu saboda annobar, kuma yanzu akwai tsoro mai yawa cewa za mu iya fuskantar irin wannan ko wanda ya fi muni''.

Desert locusts stand on the local vegetation in Ipsolo county of northern Kenya

Asalin hoton, FAO/Sven Torfinn

Bayanan hoto, Manoma da makiyaya a gabashin kenya na fargabar me zai faru idan farin suka dinga girma

Yanayi mai kyau

Masana sun ce tsakiyar Somaliya da gabashin Habasha sun sami sama da matsakaicin ruwan sama a lokacin damina daga Satumba zuwa Nuwamba.

Wannan yana nufin ƙasa ta gyaru, sannan yanayi ya inganta ta yadda fari za su ji dadin rayuwa.

Mista Cressman wani masani, ya ce "Wannan ya zama kyakkyawan wurin kiwo ga fari. "Kuma wadannan yankuna hakika manya-manyan wuraren kiwo ne."

Da wannan yanayi, cikin 'yan watanni' fari sun tashi daga ƙaramin al'amari sun zama babban al'amari.

Locusts covering the ground in Ceel-Gaal village, in Salal region, Somaliland.

Asalin hoton, FAO/Isak Amin

Bayanan hoto, Farin sun ta hayayyafa a Somaliya da Kenya

Rikici

Masana sun ce yawan sanya ido a yankuna da dama da abin ya shafa sun taimaka wajen nisanta farin da gari.

Amma ƙoƙarin bai kai ga gaci ba musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro. "Misali, ba a sanya ido a kudancin Somaliya," in ji Mista Cressman.

Yemen wata ƙasa ce da ke da filayen kiwo da yawa. Amma rikice-rikicen da ke faruwa na nufin sa ido ba zai yiwu ba a yankuna da dama.

Masana sun ce har ila yau, farin sun yi ƙaura zuwa Saudiyya daga Yaman.

Hakanan za su iya tsallaka Bahar Maliya akai-akai, tazarar nisan kilomita 300, saboda za su iya kasancewa cikin iska na dogon lokaci.

Goats graze in Marsabit county where there have been nice vegetation expansion due to good rains

Asalin hoton, Jeremiah Lekoli

Bayanan hoto, Manoma sun ce sun yi asarar dabbobi sakamakon barnar kwarin Farmers say they lost livestock after the last locust invasion wiped out vegetation and pastures

Feshin maganin ƙwari

Ƙasashen yankin su ma sun shirya kansu don amfani da magungunan ƙwari a ƙasa da kuma sama.

"Ayyukan daƙile su ya taimaka wajen kare tan miliyan 2.7 na hatsi, wanda ya kai kusan dala miliyan 800 a kasashen da tuni suka yi fama da matsalar karancin abinci da talauci," in ji FAO a cikin wata sanarwa.

Amma masana sun ce ana buƙatar ƙarin kudade domin kaucewa barazanarsu.

"Muna sa-ido ne amma ba a ba mu wani kayan aiki ko magungunan ƙwari don yin feshi ba," in ji Jeremiah Lekoli, wani masanin kimiyyar kare muhalli.

"Yana da matukar mahimmanci mu samu waɗannan abubuwa, in ba haka ba a lokacin da suka iso za su haifar da mummunar ɓarna.

Hukumar ta FAO ta yi gargadin cewa tuni sama da mutane miliyan 35 suka soma fuskantar karancin abinci a cikin kasashe biyar da ke fama da matsalar.

Ya ce wannan adadi na iya ƙaruwa da wasu miliyan 3.5 idan ba a yi wani abu ba don shawo kan ɓarkewar sabuwar cutar ba.