Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashen da ke aiwatar da hukuncin kisa a duniya
- Marubuci, Daga Tawagar Bin Kwaƙƙwafi Ta BBC
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Batun zartar da hukuncin kisa na daga cikin abubuwan da ke jan hankali a yanzu, bayan umarnin shugaban Amurka Donald Trump na aiwatar da hukuncin a kan mutane da dama yayin da yake shirin sauka daga kan mulki.
Mun yi duba a kan kasashen duniya da har yanzu suke aiwatar da wannan hukunci.
Ƙasashe goma na farko da suka fi yawan wadanda aka zartarwa hukuncin su ne:
- China 1000
- Iran 251
- Saudiyya 184
- Iraq 100
- Masar 32
- Amurka 22
- Pakistan 14
- Somaliya 12
- Sudan Ta Kudu 11
- Yaman 7
Karin Bayani : Babu wasu cikakkun bayanai game da China, amma ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta ce mutum dubu aka zartarwa hukuncin a ƙasar.
Mun samu waɗannan bayanai na sama ne daga rahoton ƙungiyar ta Amnesty na shekarar 2019.
Bayan China, ƙasashe uku ne ke da kaso 80 cikin 100 na yawan mutanen da aka zartar musu da hukuncin a duniya, wato Saudiyya da Iraqi da Iran.
A cewar Amnesty, China ce ta fi kowacce ƙasa a duniya zartar da hukuncin kisa a duniya.
Ƙungiyar na samun alƙalumanta ne daga hukumomi, da rahotannin kafafen watsa labarai da kuma dangi ko ƴan uwan waɗanda aka zartarwa hukuncin.
Saudiyya ce kaɗai ƙasar da ke amfani da tsarin fille kai wajen aiwatar da hukuncin kasa a duniya.
Sauran hanyoyin da ake bi sun haɗar da rataya, allurar mutuwa da kuma bindigewa.
A Amurka. jihohi bakwai sun aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar yin allurar mutuwa a shekarar 2019, sai kuma jiha guda wato Tennesee da ta aiwatar da hukuncin ta hanyar amfani da lantarki.
Jimillar mutum 25 aka yanke wa hukuncin a shekarar 2019, sannan cikin shekara 11 a jere, ita ce ƙasa ɗaya tilo da ke zartar da hukuncin kisa a yankin Amurka.
Tun daga shekarar 2013, kimanin mutum guda kasashe 33 suka aiwatarwa hukunci.
Taswirar ƙasashen da suka zartar da hukuncin kisa daga 2013-2019
Idan ka cire China, alƙaluma na nuna cewa hukuncin kisa na ci gaba da yin ƙasa tun shekarar 2015.
Mutum 657 aka yankewa hukuncin a 2019, abin da ke nufin cewa adadin ya yi ƙasa da kaso biyar idan aka kwatanta da 2018, sannan adadin ne mafi ƙaranci cikin fiye da shekaru 10 da suka gabata.
Adadin waɗanda aka zartarwa hukuncin daga 1985-2019
Adadin ƙasashen da ke soke hukuncin kisa na ci gaba da ƙaruwa sannu a hankali, daga 48 a 1991 zuwa 106 a 2017.
Babu wata ƙasa a duniya da ta soke hukuncin na kisa a shekarar 2019, amma Amnesty ta ce akalla ƙasashe 145 na duniya ne suka daina amfani da hukuncin a aikace, ko kuma sun soke shi baki ɗaya.
Ƙasashe nawa ne suka soke hukuncin kisa?
Akalla an yankewa mutane 2,307 hukuncin kisa a cikin kasashe 56 a shekara ta 2019. Amma a wasu lokuta akan sauya hukuncin domin kasashen ba sa son aiwatar da shi.
A cikin ƴan shekarun nan yawan kasashen da ke zartar da hukuncin kisa ya ragu a hankali.
A cewar Amnesty akwai:
- Kasashe 106 ne waɗanda doka ba ta ba da izinin yin hukuncin kisa ba
- Ƙasashe 8 ne waɗanda suka amince da hukuncin kisa, amma a kan manyan laifuka, sannan wani yanayi na musamman, kamar waɗanda aka aikata a lokutan yaƙi.
- Kasashe 28 waɗanda suke da dokokin hukuncin kisa amma ba su zartar da hukuncin kisa ba tun aƙalla shekaru 10 da suka gabata.
- Akwai kasashe 56 waɗanda dokokinsu suka amince da hukuncin, amma ba a damu da shi ba.
Alƙalumman na ƙungiyar Amnesty sun haɗa da ƙasashe biyar, waɗanda ba mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya ba.