Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Tigray: Yadda labaran ƙarya ke ruruta wutar rikicin Ethiopia
- Marubuci, Daga Peter Mwai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
Gargadi: Wannan labarin yana dauke da hotunan da wasu mutane ba za su ji dadin kallonsu ba
A yayin da gwamnatin Ethiopia take kai hare-haren soji a yankin Tigray da ke arewacin kasar, wasu mutane na amfani da wannan dama wajen watsa labaran karya a shafukan intanet.
Abubuwan da ake yaɗawa sun haɗa da hotuna da bidiyon da ba su da dangantaka da rikicin, a wani lokaci kuma sai a juya shi don ya yi kama da rikicin.
Wani hoton makamin roka da aka yi wa kwaskwarima
Akwai mutane da dama da suka rinƙa yaɗa wani hoto da ke nuna cewa an yi amfani da wani makami mai linzami ƙirar S-400 na Rasha wurin kai hari a yankin Tigray.
Sun kuma yi iƙirarin cewa an yi amfani da wani makami na jefa wuta a yankin.
Wani rubutu da aka wallafa tare da hoton ya ce "Wannan makamin ko Ethiopia a matsayinta na ƙasa ba ta da shi.
"Yan yankin Tigray na da shi domin su kare kansu."
Hoton ya nuna sojoji cikin wani abu da ya yi kama da kayan sojoji na musamman na yankin Tigray suna tsaye a kusa.
Sai dai an sauya hoton bayan saka sojoji a ciki.
Inuwarsu na nuna wata alƙibla daban, za a ga cewa inuwar tasu na nuna kodai wani ɓangare na daban idan aka kwatanta da wasu abubuwan da ke kusa ko kuma sufa yi duhu.
A ɗaya daga cikin hotunan, sojan ya sha ban-ban da yanayin wurin da aka ɗauki hoton.
Wani bincike da aka gudanar na bin diddigin hoton ya nuna cewa an ɗauki hoton makaman yayin da ake wani atisaye na sojoji a yankin Astrakhan da ke Rasha.
Makami mai linzamin ƙirar S-400 makami ne na zamani da Rasha ke ƙerawa wanda ƙasashe kaɗan ne suka saye shi.
Kuma Ethiopia ba ta cikin ƙasashen.
Ethiopia ba ta taɓa sayen S-300 ko kuma S-400 ba, haka kuma, babu wata makwabciyarta da ta taɓa saye.
Jirgin yaƙin da aka 'kakkaɓo' ba daga Ethiopia yake ba
Akwai ɗaruruwan mutanen da ke amfani da shafin Facebook da suka rinƙa yaɗa wani hoto da iƙirarin wani jirgin yaƙi na Ethiopia na ƙonewa a ƙasa bayan an harbo shi.
Wani daga cikin saƙon da aka wallafa ya ce: "An kai hari ga dakarun Tigray na musamman ta sama.
"Sun lalata jirgin yaƙin Ethiopia guda tare da kashe jami'an sojoji da dama.
"Ana ci gaba da rikici."
Sai dai wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa asalin hoton ba daga Ethiopia yake ba.
Ko da aka duba domin gano lokacin da aka fara wallafa hoton, ga abubuwan da muka samu:
- A watan Yulin 2018, kafar watsa labarai mallakar Iran wato Press TV ta kawo wani rahoto na jirgin yaƙin Saudiyya da aka harbo a Yemen inda aka yi amfani da wannan hoto.
- Haka ma a watan Mayun 2015, an bayar da rahoton wani jirgi ƙirar MiG-25 da aka kakkaɓo a kusa da birnin Zintan na Libiya.
Amfani da hotunan hatsarin jirgin Boeing 737 Max na Ethiopia
Wasu mutane da dama sun riƙa yaɗa hotunan hatsarin jirgin ɗaukar fasinja na Boeing 737 Max mallakar Ethiopia wanda ya yi hatsari bayan ya tashi daga Addis Ababa ya kashe mutum 150 a Maris ɗin bara.
A wani hoto da aka wallafa a Facebook wanda tuni aka goge shi, ya yi iƙirarin cewa gawarwakin da ke cikin hoton kusa da yankin Tigray na sojojin ƙasar ne daga yankin Amhara.
Akwai sojoji da dama a yankin na Amhara da ke yaƙi tare da sojoijin Ethiopia.
Sai dai wasu daga cikin masu amfani da shafin na Facebook sun fito ƙarara sun bayyana cewa waɗannan hotunan ba su da alaƙa da abin da ke faruwa a yankin na Tigray.
Babu ministan Ethiopia da ya buƙaci sojoji su saka takunkumi
An ta yada wani saƙo da ake iƙirarin cewa minstar lafiya ta ƙasar, Lia Tadesse ce ta wallafa shi inda aka ce ta ce ta zayyana wa sojojin da ke yaƙi ƙa'idojin da za su bi wajen kare kansu daga cutar korona yayin yaƙi.
Fassarar abin da aka rubuta na nuna cewa: "Tare da bayar da tazara, da amfani da sanitiza da kuma saka takunkumi, muna neman duka masu ruwa da tsaki su taimaka wurin kawo ƙarshen wannan rikici."
Sai dai wannan saƙon an haɗa shi ne.
Haka kuma wannan saƙon na Twitter babu shi a shafinta na Twitter.
Bincike ya kuma nuna cewa duk wasu saƙonnin da take wallafa a shafinta na Twitter tana amfani da iPhone ne ba Android ba.