Me ya sa kunne ke motsi idan ana cin wani abu?

    • Marubuci, Lucía Blasco
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo

Sauti abu ne da ake kira "ɗanɗanon da aka manta".

Charles Spence, wani mai nazari ne kan halayyar dan adam a Jami'ar Oxford, da ya ce ba da bakinmu ko idanunmu ba ne kaɗai muke jin dadin abinci ba - har ma da ta hanyar amfani da kunnuwanmu.

Jin ɗadin tauna abinci mai kayau-kayau shi ma yana matukar nishandantar da shi.

Ya shafe kusan shekaru ashirin yana gudanar da bincike kan yadda kwakwalwarmu ke sarrafa yanayin sadarwa tsakanin duka hanyoyin isar da sakon dan adam, musamman lokacin cin abinci.

"Sautin rumurmushewar abinci, sautin zuba abinci, ƙarar cokali na kankarar farantin cin abinci, ko kuma ma irin wakokin da mukan saurara lokacin cin abinci, '' ya shaida wa BBC,'' suka karar na shafar yadda muke cin abincin.''

"Wasu fiye da wasu,'' ya ƙara cewa.

Me ya sa kunne ke motsi idan ana cin wani abu?

Spence marubucin littafi ne mai suna Gastrophysics: da aka yi wa laƙabi da kimiyyar cin abinci, kuma daraktan ɗakin bincike na Crossmodal na Jami'ar Oxford ne.

Ya yi hadin guiwa ne da wasu fitattun masu dafa abinci ne, da suka haɗa da Ferrán Adriá na kasar Spain da Heston Blumenthal na ƙasar Burtaniya, don haɗa nau'ukan abinci ta hanyar fasaha daban-daban.

Masanin kimiyyar ya yi amanna cewa cin abinci wani abu ne mai cike da sarƙaƙiya fiye da saninmu, musamman a matakin gwaji ko kuma jarrabawa.

Kuma ba shi kaɗai ne yake da wannan tunani ba.

"Akwai abubuwa da dama da ke saka mu farin ciki da abinci: kamshi, kyau, dandano da kuma sauti,'' in ji wata kwararriya kan harkar dafa abinci Amanda Miles-Ricketts ta bayyana.

"Kuma babu wani abu mai gamsarwa kamar abu mai ƙayau-ƙayau.''

Bincike kan ƙayau-ƙayau

Akwai nau'ukan abinci da dama masu ƙayau-ƙayau, daga wadanda aka sarrafa a masana'antu kamar su ƙananan biskit da kuma garin kunun karin kumallo da kuma nau'ukan gyaɗa.

Charles Spence na shirin gudanar da bincike kan ko dandanon ƙayau-ƙayau din dankalin Turawa zai fita daban idan muka sauya yadda ake sarrafa shi.

Ya sarrafa sautin ƙayau-ƙayau din ta yadda zai ja hankulan mutane a kan cewa wasu abinci sun fi wasu yin ƙayau din.

Waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen gudanar da binciken sun ɗandana kashi biyu na dankalin Turawan da aka sarrafa zuwa ƙayau-ƙayau, amma su bayar da bayanin bambancin ɗanɗano a lokacin da aka ƙara sauti na wucin gadi.

Jami'ar Harvard ta bai wa Spence lambar yabo ta an "Ig Nobel" kan wannan bincike - lambar yabo mai alfarma.

Amma kuma, kimiyyar abinci mai ƙayau-ƙayau gagarumin abu ne.

"Lokacin da muka gudanar da binciken a shekarar 2009, akwai shakku game da ko hakan sakamakon zai kayatar,'' ya bayyana.

"Amma tun bayan wannan lokaci, an gudanar da bincike daban-daban don kwatanta sautuka da ƙamshi.''

Karfin sautinsa, yanayin kayunsa

"Yawanci abincin da ake sarrafawa na gaggawa su kan kasance masu ƙayau-ƙayau, kusan ko wannne kan fitar da sauti,'' kamar yadda Spence ya ce.

"Babu wanda ke son soyayyen dankalin Turawa mai laushi, duk da cewa mun san yana ƙunshe da duk sinadaran da ke ba shi ɗanɗano da kamshi.''

Har yanzu batun ko me yasa muka fi son abinci mai ƙayau-ƙayau ya kasance cikin lalube, amma akwai wasu rubutattun bincike da za su bayyana hakan, kamar yadda Charles Spence ya bayyana.

"Wani saƙo ne mai zuwa cikin sauri a ƙwaƙwalwarmu,'' ya ce.

Kayan marmari da sautinsu ya fi fita sun fi kyau, don haka muke danganta yanayin sautinsu a matsayin wani abu mai kyau da kuma karin lafiya.

Haka ma abinci mai ƙayau-ƙayau kamar kananan biskit, da soyayyan abinci - masu ɗauke da maiko mai yawa.

Kwakalenmu in ji Spence, "na buƙatar" nau'ikan abinci masu bayar da kuzari - gaskiyar magana, akalla kashi 60 bisa dari na ita kan ta ƙwaƙwalwa na ƙunshe da maiƙo ne.

"Hakan wata manuniya ce kan dalilan da suka saka muke ƙaunar sautin ƙayau-ƙayau'', ya ce.

Amma ƙwararriya a fannin abinci Amanda Miles-Ricketts ta damu.

"Abinci wanda babu kiwon lafiya a tare da shi, kuma aka fi mutuwar so galibi su ne masu ƙayau-ƙayau,'' ta jaddada, '' wannan ba wai gamo da katar ba ne.''

Spence ya sake jera wasu bayanai kan daluilan da suka sa muke son ƙayau-ƙayau.

"A lokacin da muka fara cin wani abu muka kuma ɗanɗana, ƙwaƙwalwarmu kan ji kuma ba ta daina so'', ya ce.

"Amma idan kana cin wani abu mai fitar da sauti, sautin kan ja hankalinka kan abin da ke cikin bakinka.''

Hakan na nufin cewa mun fi ƙaunar abinci mai fitar da sauti saboda muna jin ƙamshinsa ya fi daɗewa.

Amma abin tambaya game da hanyoyin aike wa da saƙonnin jikinmu - cin abinci ya wuce batun fitar da sautin ƙayau-ƙayau.

Kamar yadda sauti ke shafar danɗano, haka ma kida.

A lokacin da sauti ya zama ɗandano

Spence da tawagarsa sun gudanar da bincike kan dangantaka tsakanin kida da kuma dandanon abinci.

Sun yi amanna cewa abinci mai ɗanɗanon zaƙi da tsami na da dangantaka da sauti mai karfi, kana dandanon daci daidai yake da sauti marar amo.

" Idan misali, ka saurari waƙa a yayin da kake shan shayi ko kuma cin alawarcakulet, hakan ka iya kara ɗanɗanonsu,'' Spence ya ce.

Miles-Ricketts ya bayyana cewa masana'antun sarrafa abinci na ƙara yin la'akari da cewa cin abinci abu ne da ke bi ta kafofin aikewa da sakonni jikin dan adam daban-daban.

Yayin da akwai fargabar cewa za a iya amfani da hakan jirkita tunanin masu sayen abinci zuwa cin abincin da bai dace ba,'' za kuma mu iya amfani da sauti da kida wajen cin abinci mai ƙara lafiya,'' in ji Charles Spence.

"Za mu iya cin abincin da babu sukari sosai idan muka saka 'kiɗa mai daɗi' don kara dandanon abincin, a maimakon kida mai karfi a wasu gidajen cin abincin, da yawanci kan rage yadda muke jin dandanon abincin.''

"Kamar yadda muke haɗa wasu nau'ukan abinci nau'in wata barasa, za mu iya haɗa ɗanɗano da kuma sauti,'' ya ƙara cewa.

Masanin kimiyyar ya ce akwai wata sabuwar hanyar da za a iya sake bi.

"Mutane da dama ba za su taɓa tunanin cewa kida zai iya sauya ɗanɗanon abincin. Me zai hana mu haɗa dandanon da kuma sautin?''

''Ba abin damuwa ba ne kana iya sauraron ko wane irin kiɗa: akwai ɗanɗanon da zai iya tafiya sosai da shi,'' ya ƙara da cewa.