Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gidan Arewa: Kayan tarihi da al'adun arewacin Najeriya
Gidan tarihi na Arewa (Arewa House) da ke garin Kaduna a yankin arewa maso yammacin Najeriya, cibiya ce da ke tattara tarihin Marigayi Ahmadu Bello Sardaunan Arewa da kuma tarihi da al'adu da sana'o'in yankin.
An kafa cibiyar ne bayan kisan gillar da aka yi wa Firimiyan Arewa na farko Sardauna, a juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 1966.
Sojojin sun tayar da bam, suka kuma kashe Sardauna da matarsa da ma'aikatansa a wannan gida. A juyin mulkin ne aka kashe Firaministan Najeriya na farko Abubakar Tafawa-Balewa.
Yanzu Gidan Arewa, wanda shi ne asalin gidan Sardauna, shi ne Cibiyar Bincike da Adana Tarihi na Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, Najeriya.
Asali da tarihi
"Gidan hukuma ne da aka mayar gidan tarihi domin tunawa da rayuwar Sardauna da mazajen ƙwarai da aka yi a lokacinsa," in ji Rabi'u Isah Hassan, Mataimakin Shugaban Gidan Tarihi na cibiyar.
A shekarar 1970 ne cibiyar ta fara aiki domin kiyaye tarihin Arewacin Najeriya da shugabannin da suka kafa yankin.
Cibiyar na da nufin bai wa masu tasowa damar ganin yadda yankin ya zauna a dunƙule har zuwa sanda aka raba shi gida shida a 1967.
An fara gina gidan Sardauna ne a shekarun 1950 a matsayin gidan gwamnati na Firimiyan Arewa wato Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.
A zamanin Sardauna ma an yi wani shiri na musamman kan tattali da adana tarihin Arewa, karkashin wani masani dan kasar Ingila, Farfesa HFC Smith, wanda ya dukufa wurin tattarowa da rubuta tarihin yankin.
Gabanin kammala aikin ne aka yi juyin mulkin 1966, abin da ya kawo tsaiko, kafin daga baya a ci gaba da aikin.
Wane ne ya mallaki Gidan Arewa?
Bayan an raba Jihar Arewa zuwa jiha shida, an kafa hukumar kula da hidimomin da ƙadarorin da jihohin suka gada daga tsohuwar jihar Arewa.
Ƙadarorin sun haɗa da Jami'ar ABU wadda ta ci gaba da zama ƙarƙashin jihohin har zuwa sanda Shugaba Murtala Muhammad ya mayar da ita mallakin gwamnatin tarayya.
A ƙarƙashin hukumar ne aka kafa Gidan Arewa a 1970, domin ci gaba da aikin adana tarihin da aka riga aka faro a baya.
"Don haka sai magabata suka sa Gidan Arewa a ƙarƙashin Jami'ar ABU, kuma har yanzu a ƙarƙashin jami'ar take."
Ayyukan farko
A shekara 10 na farkon Gidan Arewa, Daraktan cibiyar na farko kuma ma'aikacin Sashen Tarihi na ABU, "ya horas da malamai ko ɗaliban tarihi da ko wanne aka ba shi fannin da zai ƙware a kai, musamman ma yankuna ko lardunan da suka fito."
Smith ya kuma jagoranci buga ayyukan tarihin Arewa kuma har yanzu a kan wannan baka ake.
Dalilin kafa Gidan Arewa a Gidan Sardauna
An mayar da gidan Sardauna zuwa gidan tarihi ne saboda muhimmancinsa a matsayin gidan gwamnatin Arewa, da nufin nuna wa na baya yadda shugabanni na gari suka rayu da irin ayyukan alheri da suka yi wa Arewa.
Sunan unguwar da gidan yake a wancan lokaci Nasarawa ko Unguwar Ministoci saboda a nan ministocin Arewa da aka fara yi suke zama.
A unguwar ce kuma aka yi gidajen da wakilan lardunan Arewa 12 suke zama idan suka zo halartar zaman Majalisar Arewa a Kaduna, bayan fara siyasa a Najeriya a 1954.
Ministoci da Sardauna a matsayinsa na Firimiya sun ci gaba da zama a rukunin gidajen.
Amma saboda a mayar da gidan firimiya daidai da matsayinsa, "…daga baya sai aka yi katanga, domin da gidan ba shi ma da katanga, a buɗe yake kamar sauran gidajen ministocin," in ji Rabi'u.
Sardauna ya ci gaba da zama a gidan har daren Juma'a wayewar garin Asabar 15 ga watan Janairu 1966, da aka yi juyin mulki. "A nan ya rasa ransa tare da mai ɗakinsa Hafsatu da wasu barorinsa."
Me ya sa ake ce masa Gidan Arewa?
An ba cibiyar suna Gidan Arewa ne domin ta kasance gida ga duk mutumin yankin ko mai nasaba da ita, duk da cewa an ƙirƙiri jihohi daga asalin jihar Arewa.
"Amfanin tarihi shi ne ya nuna inda aka yi tarayya. Haɗin kan da ke tsakanin jama'ar Arewa ne ya sa aka ce masa 'Gidan Arewa'."
Abubuwan tarihi
Kayan tarihin da ke wannan cibiya sai wanda ya gani, duk da cewa ba mu samu damar ɗaukar hotuna yadda muka so ba.
Wurin da aka kashe Sardauna
Daga cikin abubuwan tarihi da ke Gidan Arewa akwai 'inda aka samu gawar Sardauna, wanda yanzu aka killace domin nuna alama.
"Ba a cikin gidan aka binne shi ba, saboda a lokacin an sa dokar hana fita a fadin Arewa.
"Sai dai aka kira Sarkin Musulmi na wancan lokaci, Abubakar III, aka gaya masa halin da ake ciki. Shi kuma ya ba da izini a rufe Sardauna a gidansa da ke Unguwar Sarki."
Kayan Sardauna
Mun samu damar shiga falon Sardauna inda muka ga kayan da ya yi amfani da su. Mun ga agogonsa da darduma da carbi da littafin addini.
Akwai kuma lasisin tuƙi da makullin alfarma da Hukumar Kula da Gidaje ta ba shi a lokacin bikin buɗe Babban Bankin Najeriya (CBN).
Mun kuma ga hotuna da rediyo mai batir da kujeru da teburin tsakar daki da matashi da sauran kayansa ciki har da manya rigunansa.
Ofishin Sardauna
Har yanzu ofishin da Sardauna ya gina mai suna 'Marble Office', a gidan gwamnati na Gidan Arewa. Yanzu 'Marble Office', shi ne ofishin shugaban cibiyar.
Teburin Sardauna
Teburin da ke ofishin Sardauna na nan har yanzu, ɗauke da kundayen gudanar da gwamnati. Teburin na cikin babban zauren kayan tarihin cibiyar.
Filin Wasa
Har yanzu filin wasan 'Fives' da Sardauna ya yi na wurin da aka fara kafa shi a bayan gidansa, jama'a suna amfani da shi.
Kayan gargajiya
A cikin zauren akwai kayan tarihi da na gargajiyar Arewa da na ɗaiɗaikun jihohi.
Sassan da ke Gidan Arewa
Sassan Cibiyar Bincike da Adana Tarihi ta Arewa sun hada da:
Gidajen tarihi
Matattarar kayan tarihi da hotuna da kayan sana'a da kuɗaɗe da suturu da kayan amfanin magabata.
Gidan tarihi na farko da ke Gidan Arewa shi ne gidan da Sardauna ya zauna. Bayan sojojin da suka yi juyin mulkin sun ƙona rufin gidan, daga baya an gyara shi, aka mayar da rufin sannan aka mayar da abubuwan da suka ƙone yadda suke.
"Ana kuma zuwa ziyara domin a ga yadda Sardauna ya rayu rayuwa mai sauki."
Na biyu shi ne gidan tarihin jihohin Arewa 19 da baje-kolin yadda aka samar da yankin Arewa daga lokacin Turawa a 1900 har zuwa sadda aka yi juyin mulkin 1966.
Gidan tarihin jihohin Arewan na da babban zauren kayan tarihin jihar Arewa. Akwai kuma ƙananan zauruka da aka ware na al'adu da sarakuna da arzikin da Allah Ya hore wa daidaikun jihohin yankin.
Kasancewar an kaddamar da zaurukan ne a 1995 kafin jihohin yankin su zama 19, ya sa kayan tarihin wasu jihohin yin tarayya a zaure guda, bayan an kara jiha uku a yankin a 1996.
Ɗakin Karatu
Rabi'u ya ce ɗakin karatun cibiyar na da litattafai masu wuyar samu a fadin Najeriya.
"Litattafai ne da suka yi magana tun daga lokacin zuwan Turawa da shekara 60 da suka yi mulki a Arewa."
Ma'adanar takardun tarihi
Sashe ne a cibiyar da ke adana takardun tarihi (fayil) da Sardauna ya yi amfani da su a lokacin yana Firimiya.
A wannan sashe akwai kundayen gwamnati da yadda ake tafiyar da sha'anin mulki, daga lokacin Turawa har zuwa ita jihar Arewa da lardunanta da kuma takardun ofishin Firimiya.
"Mutum zai ga yadda aka gudanar da mulki da yadda wadannan larduna guda 12 suka wanzu a wancan zamani da yadda ake tafiyar da sha'anin mulkinsu."
Sashen binciken tarihi
Akwai ƙwararru da ɗalibai da suka ƙarancin ilimin tarihi da ke gudanar da duk binciken tarihi da zai iya tasowa.
Su ke taimaka wa masu bincike da suka zo cibiyar game da binciken da suka zo yi.
"Tarihi abu ne da ya riga ya gabata, sannan akwai hanyoyi da ake bi ake tattaro shi a kuma adana shi. Tilas sai mutanen da suka san fannin da kuma dabaru da hikimomi da ake bi don yin wannan."
Yadda aka tara kayan tarihin
An samu litattafai da takardu da sauran kayan tarihi da adana a Gidan Arewa ne daga kayan da aka gada daga gwamnatin jihar Arewa.
Daga ciki akwai kayan da Sardauna ya yi amfani da su a ofishinsa ko a gidan gwamnati, ko a gidansa da ke mahaifarsa a garin Rabah da ke jihar Sokoto.
Akwai kuma rubuce-rubucen da Turawa suka yi kan Arewa da Najeriya a tsawon mulkinsu, wadanda aka ajiye a gidan gwamnati.
Daga cikin mutanen da suka yi zamani da Sardauna ma, wasu kan kawo wa cibiyar gudunmuwar kayan tarihi.
Wasu kuma masana da manyan mutane ne ke barin wasiya cewa idan sun rasu a kawo su cibiyar.
Sashen kula da al'adu da tarihi a jihohi ma kan tattaro sannan su kawo wa Cibiyar irin wadannan kaya.
Gidan na kuma saye da ajiye karin wasu kayan tarihi da suka shafi Arewa.
Wasu ɓangarorin Gidan Arewa sun hada da:
Ɗakin taro
Bayan karamin dakin taron da ke kusa da ofishin Sardauna a zamaninsa, an gina wasu manyan dakuna da zaurukan taro a Gidan, "domin cibiyar ta zama mahada ta musayar ra'ayi da ilimi ta Arewa."
Ɗakuna
Akwai kuma dakuna domin masu bincike daga ciki da wajen Najeriya. Gidan Arewa mahaɗa ce kuma rumbun tunani na yankin.
Gidan ya zama sakatariyar shirin bunƙasa ilimi a Arewa inda kwamishinonin ilimin jihohin yankin ke tattauna yadda za a ciyar da ilimi gaba.
Ana kuma gudanar da taruka ko shirya bincike na musamman kan bunkasa tsaron yankin a cibiyar.
Wasu daga cikin yunkurin kan taso daga cibiyar, sannan ta gayyato jihohi su mara baya kan yadda za a yi aikin.
Wani lokaci jihohi ne ke neman Gidan Arewa ya shirya. Ko jihohin su shirya abinsu da kansu, amma su sa Gidan Arewa ya zama mahadar da wakilansu za su tattauna abubuwan da suka shafi Arewa.
Wani lokaci ma mutane masu sha'awa daga waje ko masu wata buƙata a yankin kan yi haɗin gwiwa da Gidan Arewa domin a yi wani shiri na musamman.