Sake fasalta ƙasa: Abubuwan da kuke bukatar sani kan kiraye-kirayen fasalta Najeriya

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Batun sake fasalta kasa na daga cikin abin da ke jan hankalin 'yan kasar inda wasu ke ganin shi ne kawai mafita ga ɗumbin matsalolin da ke addabar ta.

A karshen makon da ya gabata, wani fitaccen Fasto a cocin Redeemed Christian Church of God, Fasto Enoch Adebayo yake cewa "ko a sake fasalta kasa ko kasar ta dare, domin ba lallai sai ka kasance manzo ba kafin ka iya sani ko hasashen abin da zai faru".

Sai dai waɗannan kalmomi na Fasto Adebayo da ire-irensa da aka jiyo daga bakin Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi da tsohon gwamnan Cross Ribas kuma tsohon ɗan takarar shugabancin kasa, Donald Duke da tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili ya fusata fadar shugaban kasa.

Mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafafen yada labarai, Malam Garba Shehu ya ce irin waɗannan kiraye-kiraye da ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi ke yi kan fasalta kasa da sunan ceto ta, ba abu ne da za a amince da shi ba kuma ya saɓa nuna kishi ga kasa.

Malam Garba ya ce wannan kawai wani yunkuri ne na sake jefa kasar cikin barazana da hadarin da dama take ciki da ingiza al'umma.

Amma masana harkokin siyasa kamar Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce a komai ba a rasa alfanu da rashinsa, sai dai a duk lokacin da irin wannan batu ya taso ba a rasa son zuciya a ciki.

Wannan layi ne

Me sake fasalta ƙasa ke nufi?

A tattaunawar da muka yi da Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce, batun sake fasalta kasa abu ne mai dogon tarihi tun kafin samun yancin kai ake wannan zancen.

Amma babu wata taƙamaimiyar ma'ana kan abin da ake nufi, sai dai akwai wasu abubuwa kamar uku da suka jima a tarihi ana danganta fasalta kasa da su.

1. Tattalin arziki

Na farko akwai wadanda ke ganin sake fasalta kasa da nufin sauya tsarin tattalin arzikinta, ɓangaren da ake samun arzikin ƙasa su riƙe abinsu, sai dai kawai su ɗan san wa gwamnatin tsakiya.

2. Tsarin tarayyar gaskiya

An sha yin kiraye-kiraye kan sauya tsarin da ake kai, a koma yadda gwamnatin jihohi za su fi ƙarfin na tarayya, ma'ana za su ke cin cikakken 'yancin gashin kai ba tare da uzurawar ko jiran gwamnatin tarayya ba.

3. Kabilu

Akwai batun ƙananan ƙabilu da ake cewa ya kamata a yi musu tsari ko a tabbatar manyan ƙabilu ba za su iya danne su ba.

Wannan layi ne

Me yasa batun ke jan hankali a yanzu?

Map

Kusan ana iya a cewa wannan kira a yanzu bai sauya daga wanda aka sha ji a baya ba, ta wani ɓangaren ko fuska guda ya tafi da tarihi, domin akwai wadanda ke maganar tsarin tarayyar gaskiya wasu na maganar ake kewaye da tsarin shugabancin.

Batutuwan da suka yi wa kasar ƙatutu kamar rashawa, matsalar tattalin arziki da tsaro na daga cikin abubuwan da masu wannan kira ke bayar da misali wajen kare hujjarsu.

Sai dai Farfesa Kamilu Fagge ya ce duk lokacin da irin wannan magana ta taso idan aka bincika akwai son zuciya irin ta siyasa a ciki, musamman ga waɗanda ke ganin ba a damawa da su a mulki.

Alfanu ko rashin alfanun

Masu maganar raba kan kasa dama abin da suke magana shi ne rage ƙarfin gwamnatin tarayya ta tsakiya a ƙarfafa jihohi da tattalin arziki, sannan komai ya daina kasancewa daga tsakiya zai fito, sannan a ƙara wa jihohi ayyuka.

Don haka farfesa Kamilu na ganin hakan zai iya rage tashin-tashina amma ba zai kawo karshen matsalar kasar ba saboda kowanne dan siyasa da zarar ba shi ke mulki ba burinsa shi ne kirkirar matsaloli kuma duk kyan abin da aka yi idan ba shi ne a Mulki ba to babu abin da ke gamsar da shi.

"Duk wadanan surutai ne da idan lokacin zabe ya soma karatowa ake bijiro da shi, yanzu da zaran anyi zaben 2023 maganar zata lafa, sai kuma bayan wasu shekaru sai su sake dako zance.

''Akasarin masu wannan abu ba wai kasar ta dame su ba ne da al'ummarta, kawai wani buri ne nasu, kuma da zarar burinsu ya cika sai su jingine batun, amma idan ba sa cikin gwamnati ba sa kan madafun iko su ne a kan gaba wajen irin wadannan surutai".

Wannan layi ne

Buƙatar Sulhu

Sardaunan Sokoto

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sardaunan Sokoto ne Firimiyan arewacin Najeriya bayan karɓar ƴancin kasar

Daya daga cikin abun da ke kashe kasa shi ne son zuciya irinta 'yan siyasa da a galibin lokuta ba sa bijiro da ƙorafi ko batutuwa sai sun ga basu ne akan Mulki ba, in ji Farfesa Kamilu.

Farfesa Kamilu ya ce tunda matsalar ta jima ana magana a kai kuma taki ci taki cinyewa, akwai bukatar a hau teburin sulhu domin warware matsalar a siyasance.

Masu ruwa da tsaki a zauna a tunkare abin a warware shi gabagadi domin idan za a cigaba da share shi ba a kula shi abin ba zai kawo ƙarshe ba zai ci gaba da haifar da rigingimu.

Ferfesa ya bayar da misali da maƙwaftan kasar Nijar, da suka shirya taron hadin-kan kasa kuma suka ɗau hukuncin daya dace domin kaucewa makamanciyar wannan rigingimun.

Karin haske

Bayan samun 'yancin Najeriya a 1960, da farko an kasafta kasar shiyya uku wato yankin yammacin na Yarbawa mai Firimiya Obafemi Awolowo, sai yankin Gabashi na kabilar Igbo mai Firimiya Nnamdi Azikwe, sai kuma Yankin Arewaci da ke karkashin Firimiya Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

Yankin arewa ya fi yawan kujeru a majalisa kuma rinjaye ya zarta a hade 'yan majalisar gabashi da yammaci.

Kusan shigen wannan tsarin ke yawo a kawuna masu neman a sake fasalta kasa, ya kasance ko a matakin jihohi ko shiyya kowa an ba shi ƙarfi da 'yanci ba wai ci gaba da zama karkashin gwamnatin tsakiya ba ko tarayya.

Sai dai salon dimokraɗiyya da tsarin da kasar ke gina kanta a yanzu irin wannan hange tamkar nema raba kasa ne kamar yada wasu masu hasashen ke cewa.

Masana dai a ko da yaushe na cewa hakan ba za ta taɓa kasancewa mafita ga matsalolin kasar da ke neman ci gaba ba.

Wannan layi ne