Muhawarar Trump da Biden: Warware ƙarya da gaskiyar kowanne ɗan takara

Donald Trump and Joe Biden

Asalin hoton, AFP

Shugaba Trump da ɗan takarar da ke kalubalantar sa na jam'iyyar Democrat Joe Biden sun fafata a muhawarar farko cikin muhawarori uku da za su yi a kafar talbijin gabanin zaɓen ƙasar da za a gudanar a watan Nuwamba.

A lokacin zazzafar muhawarar da aka kwashe minti 90 ana tafkawa, 'yan takarar biyu sun fafata kan kusan komai daga kan halin da tattalin arziki ke ciki zuwa yadda ake tunkarar cutar korona. Sashen bin diddigi na BBC Reality Check ya duba ikirarin da kowannensu ya yi, ya fito da gaskiyar kowanne kalami

Section divider

Trump: "Mun samar da tattalin arziki fiye da kowanne lokaci a tarihi"

Amsa: Wannan ikirari ba gaskiya ba ne - an samu lokacin da tattalin arzikin Amurka ya yi bunkasar da ta fi wadda shugaban kasar ya fada.

Kafin barkewar cutar korona, ShugabaTrump yayi ikirarin bunkasa tattalin arzikin da ba a taba yi ba a tarihin kasar.

A baya tattalin arzikin Amurka ya bunkasa fiye da a zamanin Trump
Bayanan hoto, A baya tattalin arzikin Amurka ya bunkasa fiye da a zamanin Trump

Gaskiya ne cewa tattalin arzikin Amurka yana bunkasa sosai kafin annobar korona - kuma hakan ci gaba ne daga abin da Gwamnatin Obama ta yi - sai dai akwai lokacin da tattalin arzikin ya fi bunkasa fiye da na wannan lokaci.

Section divider

Biden: "Mu ne kasa ta 4 mafi yawan jama'a a duniya, [amma] muna da kashi 20 na yawan mace-mace"

Amsa: Wannan ikirarin yana da kamshin gaskiya. Amma idan muka kwatanta yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar koronada yawan al'ummar kasa, akwai kasashe da dama da suka fi Amurka yawan wadanda suka mutu.

Mr Biden ya soki Shugaba Trump kan rauninsa wajen tunkarar cutar ta korona.

Alkaluman da aka bayyana sun nuna cewa ikirarinsa na da kamshin gaskiya. Al'ummar Amurka sun kai miliyan 328, wanda da kadan suka fi kashi 4 na yawan al'umar duniya biliyan 7.7.

Joe Biden

Asalin hoton, Reuters

Alkaluman baya bayan nan da Jami'ar John Hopkins University ta fitar sun nuna cewa mutum 205,942 suka mutu sanadin kamuwa da cutar korona a Amurka. Kazalika mutum 1,004,808 a fadin duniya.

Hakan na nufin, Amurka ce ke da kashi 20 cikin 100 na dukkan mace-macen da aka samu sanadin Covid-19 a duniya, kodayake kasashe sun sha bamban game da yaddda suke bayar da rahoton adadin masu kamuwa da cutar.

Bayanai kan korona
Section divider

Trump: Yin zabe ta hanyar aikewa da wasiku "zai sa a yi magudin da ba a taba yi ba"

Amsa: Bincike bai nuna wata shaida cewa hakan yana haddasa magudin zabe ba, kodayake an samu magudin zaben a wasu wurare kalilan.

Ana sa ran Amurkawa da dama za su yi zabe inda za su kada kuri'unsu ta aikewa da su ta gidan wasiku saboda kaucewa kamuwa da cutar korona.

Shugaban kasar ya sha nanata cewa hakan zai haddasa magudin zabe.

An samu wasu misalai kalilan da hakan ya faru a jihohin North Carolina da New Jersey.

Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

A watan Satumba, Ma'aikatar Shari'ar Amurka ta fitar da sanarwa a kan wani lamari da ya faru a Pennsylvania inda " aka watsar da kuri'un sojoji tara" kuma ta ce an kada bakwai daga cikinsu ne "ga Donald Trump lokacin yana dan takara".

Amma duk da wannan bincike, wasu binciken da dama sun nuna babu wata babbar hujja da ke nuna an tafka gagarumin magudin zabe.

Adadin matsalolin da ake fuskanta a zaben Amurka bai wuce kashi 0.00004 da 0.0009, a cewar wani bincike da cibiyar Brennan Center for Justice ta gudanar a 2017.

Section divider

Biden: "Mutum miliyan [a Amurka] suna fama da matsalolin rashin lafiya"

Amsa: Babu wata tartibiyar amsa a kan wannan ikirari.

'Yan takarar sun yi musayar yawu kan yawan Amurkawa da ke fama da larurar rashin lafiya, wadda ka iya hana wasu daga cikinsu samun inshorar lafiya.

Mr Biden ya ce akwai mutum miliyan 100 da ke fama da larurori na rashin lafiya, amma Shugaba Trump ya ce adadin sam ba haka yake ba."

Mutum nawa ne suke fama da wadannan larurori? Babu wata tartibiyar amsa a kan hakan.

A cewar ma'aikatar lafiyar Amurka, tsakanin mutum miliyan 50 da miliyan 129 Amurkawa wadanda ba tsofaffi ba suna fama da larura daya ko fiye da haka game da rashin lafiya.

Sai dai wasu hukumomin sun bayyana alkaluma na daban. The Center for American Progress believes ta yi amannar cewa adadin ya fi haka, inda ta ce mutum miliyan 135 da ke kasa da shekara 65 ne suke fama da larurori na rashin lafiya.

Section divider

Trump: " Nan da makonni kadan za mu samu riga-kafin korona"

Amsa: Babu wani "tabbaci" kan samun riga-kafin cutar kafin karshen watan Oktoba, kamar yadda babban mai bayar da shawara ga shugaban Amurka kan riga-kafi ya fada.

Moncef Slaoui ya yi takatsantsan kan hakan a watan Satumba.

A gefe guda, Dr Anthony Fauci, babban masani na kasar kan cutukan da ke yaduwa, ya yi hasashen cewa sai a watan Nuwamba ko Disamba ne Amurka za ta san ko za ta samar da riga-kafi maras matsala.

Ya shaida wa wani Kwamitin Majalisar Dattawa a watan da muke ciki cewa watakila a samu riga-kafin da zai isa kowanne Ba'amurke nan da watan Afrilu mai zuwa.

Section divider