Fatal Arrogance: Ina da-na-sanin fitowa a fim kan ‘yan Shi’a - Yakubu Mohammed

Tauraron fina-finan Hausa Yakubu Mohammed

Asalin hoton, @YAKUBUMOHAMMED

Bayanan hoto, Tauraron fina-finan Hausa Yakubu Mohammed

Tauraron fina-finan Hausa a Najeriya Yakubu Muhammad ya ce ya yi nadamar fitowar da ya yi a wani fim wanda ke ci gaba da janyo cece-ku-ce a wasu sassan kasar.

Fim din mai suna Fatal Arrogance, bayanai sun nuna cewa an shirya shi ne domin nuna yanayin rayuwa ta wata kungiyar Musulmai a kasar ta Najeriya.

Sai dai wani hoto da aka rika yawo da shi a kafafen sada zumunta na intanet ya sa an rinka furta kalaman batanci ga tauraron, da ma sauran wasu taurarin shirin.

Abdulbaki Jari ya tattauna da tauraro Yakubu Mohammed domin jin abin da zai ce game da lamarin:

Yakubu Mohammed: Wato lokacin da aka kawo min rubutaccen labarin fim din na duba, sai na ga labari ne a kan abin da ya faru a Zaria tsakanin kungiyar Muslim Brothers da sojoji, inda aka karkashe kuma aka harbi 'yan kungiyar 'Yan uwa Musulmin. To da aka kawo min script din, har ga Allah ban taba sanin cewa akwai wani littafi ko rubutu da aka yi mai wannan sunan na "Fatal Arrogance" ba.

Sai daga baya ne na gane cewa akwai wani littafi mai wannan sunan da aka rubuta. To bayan da na karanta script din, har ga Allah ban ga batanci ba a cikinsa, domin an an bayyana abubuwan da suka faru ne a Zaria.

Sai dai ka san shi script ba lallai ba ne ya ba ka ainihin bayanin labarin da ake son fitarwa.

Wani lokaci kana iya gano akwai kuRakurai daga baya. Lokacin da aka bani aikin sai na tambaye su ko wane ne zai dauki nauyin hada fim din.

Sai aka ce wata kungiyar masu kare hakkin dan Adam ne. To ban so in yi shisshigi ba wajen tambayoyin da nayi domin idan ka faye tambaya ana iya zaton ko kana son ka karbe aikin a hannun masu shi ne.

Rawar da na taka

Yakubu Mohammed: Ni dama na fito ne a matsayin Muslim Brother wato dan kungiyar ta 'Yan uwa Musulmi wanda aka harbe ni a hannu a yayin hargitsin na Zaria. Kuma a rawan da taka na mutu. Na yi fitowa kamar sau shida cikin fim din.

Yakubu Mohammed

Asalin hoton, INSTAGRAM/Yakubu Mohammed

Dalilin shiga na fim din

Yakubu Mohammed: Ni dan fim ne, kuma ba ni aka ba aikin hada fim din ba. An kira ni ne domin in taka wata rawa a matsayina na dan wasan fim. Amma kamar yadda na fada a baya, na ga kurakurai yayin hada fim din, kuma nayi kokarin jan hankalin masu fim din domin su gyara.

Na nemi su bayyana min me yasa suka kai fim din Enugu ganin cewa mutanen da ke can ba Musulmi ba ne kuma da wuya su iya taka rawar da ta kamata da fassarar da ta dace a fim din. Sai naga kamar ina yin shisshigi ne.

To akwai wani wuri kuma da duk Musulmi idan ya gani dole abin ya daga ma hankali. Akwai wani hoto da ya dinga yawo na Mista Pete Edochie wanda ya saka kaya irin na Musulmi, ga kwalbar giya a hannunsa kuma yana tare da wata yarinya.

To ina so in wayar wa mutane da kai. Billahil lazi la ilaha illa huwa, wannan hoton ba a cikin wannan fim din yake ba. Suna shashacinsu ne kawai suka dauka kafin a ce "action!" wato bayar da umarnin fara nadar fim din.

Shin dan fim na da hurumin ya ce a cire shi daga fim ko a wani bangare na fim?

Yakubu Mohammed: Lallai akwai hurumin. Sai dai za su ce sai ka biya su abin da ake kira "damages", wato wata asara da za su yi saboda cire kan da aka yi. Kuma na ba masu hada fim din zabi guda biyu. Idan a misali suka ce ba za su gyara ba, to a shirye nake in biya su kudi domin su cire ni daga cikin fim din saboda an ce zama lafiya ya fi zama dan sarki.

Ka fuskanci wata barazana tun da wannan batun ya bayyana?

Yakubu Mohammed: Babu wata barazana. Sai dai kawai zagi da tsinuwa, kuma dole in yi wa mutane uzuri, domin duk wanda ya ga wannan halin da aka nuna kuma yaga da nasa a ciki, dole ya ji ba dadi.

Shin ka yi nadamar shiga fim din?

Yakubu Mohammed: A gaskiya na yi da-na-sani saboda da farko na shiga ne da da kyakkyawar niyya amma yadda abubuwa suka kasance za ka ji ba dadi.

Wani zai kira ka ya ce 'Haba Mallam Yakubu, me yasa ka fito a haka?' To ita harkarmu ta fim ka kan iya fitowa a boka, ka kan iya fito wa a malami, kuma za ka iya fitowa a dan sanda.

Ba laifi ba ne wannan, amma idan fim zai saba wa wasu, bai kamata ka fito ba. Abin da yasa nayi da-na-sani shi ne ba na son yin bakin suna. Na fi son duk lokacin da za ka ji suna na, nafi son ka ji wani abu ne na mutunci kuma na kyautatawa.

A tunanina, akwai mutanen da ba a yi mu su daidai ba, wanda kusan kowa ya sani. Saboda shi rai na dan Adam, bai kamata a dauke shi ba. Sai aka ga ga fim da za a yi wanda a ciki za a fayyace gaskiya kan abin da ya faru. Shi ne na ce bari in shiga.