Ƴan matan TikTok: Matasan da aka tsare saboda bidiyon 'rashin kamun kai'

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Sally Nabil
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic, Cairo
''Abin ya zo mana da mamaki. Ba ta yi wani abu ba mara kyau ba - 'yar uwata ba ta aikata manyan laifuka. Burinta shi ne ta yi fice a san ta,'' a cewar Rahma, babbar yayar Mawada Al Adham, mai ƙarfin faɗa a ji a shafukan sada zumunta, da aka yanke mata shekaru biyu a gidan kaso.
Mawada, mai shekara 22 ɗalibar jami'a ce da aka yanke mata hukuncin zaman gidan kaso kan laifin karya dokokin al'adun iyalai na ƙasar Masar.
A watan Mayun da ya gabata aka cafke ta bayan wallafa wani bidiyo a manhajar TikTok da Instagram da ke nuna tana bi bin kan wakar wani fitaccen mawaƙi da taka rawa cikin wasu haɗaɗɗun kayan gayu.
Masu shigar da ƙara sun ce ta nuna rashin ɗa'a a bidiyon.
''Mahaifiyarta ba ta iya motsawa daga kan gadonta. Kullum tana cikin kuka. Wasu lokutan tana tashi cikin dare ta tambaya ko Mawada ta dawo gida,'' a cewar Rahma.
'Ƴan matan TikTok'

Asalin hoton, Getty Images
Mawada na daya daga cikin 'yan mata biyar da aka yanke wa irin wannan hukunci na zaman gidan yari, da kuma tarar kusan dala dubu 20.
Ƴan matan biyar da suka yi fice a matsayin ''Yan matan TikTok' sun hada da wata fitacciya ita ma a shafukan sada zumunta, Haneen Hossam, da kuma wasu uku da ba a bayyana sunansu ba.
Rahma ta ce Ƙanwarta tana tallata kayan Ƙawa a shafukan sada zumutan ga manyan fitattun kamfanoni. ''Kawai dai ta kasance mai buri sosai. Ba ta da buri daya wuce ta zama jarumar fina-finai.''
A cewar Ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty, masu shigar da Ƙara sun yi amfani da hotunan 17 na Mawada a matsayin hujjojin nuna ''rashin ɗa'arta''.
Mawada ta ce waɗannan hotunan an kwashe su ne daga wayarta ba tare da saninta ba lokacin da aka sace wayar a bara.
'Me ya sa ita?'

Asalin hoton, Instagram/mawada_eladhm
A ranar 17 ga watan Agusta za a saurari ɗaukaka ƙara kuma Rahma na sa ran ƙanwarta aƙalla ta samu sassaucin hukunci.
''Me ya sa ita?! Wasu matan da ke irin wannan harka, na yin abin da zarce hakan. Babu wanda ya hukunta su,'' ta yi waɗannan tambayoyi a cikin fushi.
Mawada ta suma a lokacin da ta ji hukunci da aka yanke mata da farko, a cewar lauyanta, Ahmed Bahkiry. ''Ta shiga kaduwa sosai - ba a fayyace irin tuhume-tuhume da ake yi mata ba.''
''Gidan yari ba mafita ba ce, ko da a ce wasu daga cikin bidiyonta sun saba doka da al'adunmu,'' a cewarsa. ''Gidan yari na ɓata mutum. Mahukunta na iya musanya gidan yari da cibiyar gyara hali.''
Ƴancin bayyana ra'ayi
Masar ƙasar Musulunci ce mai tsattsauran ra'ayi, sannan wasu 'yan ƙasar na ganin akwai rashin ɗa'a a bidiyon da ake wallafawa a TikTok.
Ana ganin akwai rashin ɗa'a a bidiyon Mawada, sannan suturar da ta sa suna nuna tsiraici a shafukan sada zumunta. Wasu kuma dai na ganin 'yan matan suna irin waɗannan wallafe-wallafe ne saboda raha don haka bai kamata a kai su gidan yari ba.

Asalin hoton, Getty Images
Masu rajin kare hakkin bil adama sun yi kira da a saki matan. Suna ganin wannan kame wani ƙoƙari ne da mahukunta ke yi don tauye 'yancin ra'ayi da kuma daƙile yadda ake amfani da shafukan sada zumunta.
Tun bayan hawan mulkin gwamnatin Shugaba Abdel Fattah Sisi da ke samun goyon-bayan sojoji, a 2014 ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam na ƙasa da ƙasa ke sukar yadda ake tafiyar da wasu tsare-tsare a ƙasar.
Sun sha tsokaci a kan dubban fursunonin siyasa, ciki har da masu sassaucin ra'ayi, malaman addinin Musulunci da 'yan jarida da lauyoyin kare hakkin bil adama.
Shugaban ya dage a kan cewa babu wani fursuna da ake tsare da shi bisa son rai a Masar, kuma mahukunta na ɗiga ayar tambaya kan sahihanci rahotanin da ake fitarwa kan hakkin bil adama.
Wariyar jinsi

Asalin hoton, Instagram/mawada_eladhm
''Mata na da damar bayyana ra'ayinsu ne kawai a shafukan sada zumuta bisa sharuɗa da dokoki da kasa ta gindaya,'' a cewar Mohamed Lotfy, shugaba wata kungiya da ke fafutikar kare hakki da neman a sako 'yan matan.
Lotfy na da yaƙinin shari'ar ta fito da batun wariyar jinsi karara. ''An zargi matan ne da karya al'adun iyalai na ƙasar Masar, amma babu wanda ya taba bayani a kan waɗannan al'adu,'' a cewarsa.
Muzn Hassan, fitacciyar mai kare hakkin mata, ta yarda cewa: ''shari'ar tsantsan nuna wariya da nuna fin karfi ne,'' galibi kuma akan mata ''wanda ake ganin su kadai ne kawai za su mutunta al'adun iyalai''.
Ko da an sake su, Lotfy ya ce an tura sako mai karfi da ban tsoro ga sauran mata masu tasowa.
''Mahukunta su bayyana karara cewa: ba ka da damar fadi ko yin abin da kake so, ko da kuwa bai shafi siyasa ba. Akwai iyakokin da tsallake su akwai wuya.''
A watannin baya-baya nan, masu shigar da kara sun fitar da sanarwa da ke magana kan ''kalubale da hadari da rayuwar matasa ke fuskanta a shafukan sada zumunta''.
Masu shigar da kara sun bukaci iyaye su mayar da hankali kan yaransu, tare da cewa ''ana batar ko asasa matasa maza da mata su kaucewa hanya, a kokarin neman suna ko nasara. Suna bin haramtaciyar hanya wajen neman kudi, karerayi da sunan yancin fadin albarkacin baki''.
Matsayi da tasiri
Mawada na da mabiya sama da miliyan uku a TikTok, miliyan 1.6 a Instagram. Wasu kuma masu suka na ganin gwamnati na kokarin murkusheta ne saboda yadda take samun karin mabiya da tasirinta.

Asalin hoton, Instagram/mawada_eladhm
Tunanin wasu masu amfani da shafukan sada zumunta shi ne ko an kama waɗannan matan ne saboda wayewarsu, da kuma rashin waɗanda suka tsaya musu.
Sun ba da misalai na irin mata da iyayensu ke da hannu da shuni ko hamshaƙai da ke sama da abin da ake zargin Mawada da aikatawa amma ba a taba ko cin su tara ba.
''Yan matan da iyayensu hamshakai ne na aikata sama da haka a shafukan sada zumunta, amma saboda su sun fito daga babban gida da wuya ka ji gwamnati na tanka musu,'' a cewar Lotfy.
Kungiyar Amnesty a wani taroon manema labarai ta ce mutanen da ke da karfi a shafukan sada zumunta na fuskantar ''barazana daga mahukunta'' wanda ake ganin za su iya tasiri wajen sauyi a kasar.










