Tsaro a Borno: Boko Haram ne suka kai wa Zulum hari ba sojoji ba

Enenche

Asalin hoton, Defence HQ/Twitter

Bayanan hoto, Manjo Janar Enenche ya ce wannan zargi ne ba na wasa ba
Lokacin karatu: Minti 2

Hedikwatar tsaron Najeriya ta musanta zargin da aka yi cewa sojoji ne suka kai hari ga ayarin motocin gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zullum.

A cewar sojin, 'yan Boko Haram ne suka kai hari, ba kamar yadda ake cewa zagon kasa ne daga wajen jami'an tsaro.

Mako guda kenan cif da wasu masu dauke da makamai suka bude wuta kan ayarin gwamnan lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa garin Baga domin wata ziyarar aiki.

Sai da aka shafe mako daya kafin rundunar sojin kasar kafin su mayar da martani kan wannan zargin da suka kira mai nauyi a bainar jama'a, duk da yadda gwamnan ya sha fada yana nanata zargin nasa.

Yayin wata hira da gidan talabijin din Channels mai zaman kansa a Najeriya, babban jami'in watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar John Enenche ya ce sakamakon binciken da suka yi kan bidiyon harin, ya nuna cewa mayakan Boko Haram ne suka kai shi, ba sojojin kasar ba kamar yadda gwamma Zulum yake zargi ba.

"Don haka mun yi bincike kan bidiyon nan take kuma mun gano cewa sashen tsara dabarun yaki bai da hannu a ciki,", in ji Manjo Janar Enenche.

Ya kara da cewa "Mun yi wa bidiyon nazari na tsanaki. Ko daga karar harbe-harben, za ka fahimci cewar ba karar irin makaman da muke amfani da su bane. Idan ka jima kana fada da abokin gaba to za ka kai matakin da duk wasu halayensa za ka fahimcesu".

Janar Enenche ya kara da cewa masu ruwa da tsaki a lamarin za su dauki mataki kan wannan batun.

'Zulum ya fusata'

A ranar 30 ga watan Yuli bayan an kai harin, gwamnan jihar Borno ya nanata cewa ƙoƙarin murƙushe ƙungiyar Boko Haram na shan zagon ƙasa daga wani rukuni na jami'an tsaron ƙasar.

THEGOVERNORBORNOFACEBOOK

Asalin hoton, THEGOVERNORBORNOFACEBOOK

Bayanan hoto, Gwamna Zulum ya ce ba zai yi shiru ba ana ci gaba da kashe al'ummarsa

Babagana Umara Zulum ya ce ba zai iya yin shiru cikin yanayi na kashe-kashe ba, saboda rantsuwar da ya yi tsakaninsa da Allah a kan zai kare al'ummar jiharsa.

Wannan na zuwa ne yayin da jihar Borno ke ganin ƙaruwar hare-haren 'yan ta-da-ƙayar-baya.

Gwamnan dai ya ce akwai buƙatar Shugaba Muhammadu Buhari ya san cewa zagon ƙasan da ake yi daga cikin harkar tsaro na kawo cikas a ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin 'yan Boko Haram bayan an shafe sama da shekara goma ana fafatawa dasu.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Zulum ya yace "Akwai zagon ƙasa cikin harkar nan wadda ba za ta bari a kawo ƙarshen rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya ba. Shugaban ƙasa ya kwan da sanin wannan muhimmin batu".

Bugu da ƙari, ya kuma bayyana damuwa game da yawan mutanen da rikici ya raba da muhallansu a Borno, ya nunar cewa akwai buƙatar mutane su koma wuraren da aka samu wani yanayi na zaman lafiya.

Wannan lamarin ya janyo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta a kasar inda wasu ke sukar salon tsaron Najeriya.

Kauce wa YouTube
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube