Yadda yawan al'ummar Najeriya zai shafi tattalin arzikinta nan gaba

Wani bincike da masana daga Jami'ar Washington suka gudanar ya yi gargaɗin cewa ƙasashen duniya ba su shirya ba game da raguwar al'umar duniya da za a samu, wanda kuma ka iya "haifar da damuwa".

Masanan sun bayyana cewa kusan kowacce ƙasa za ta fuskanci raguwar adadin al'umarta nan da ƙarshen ƙarni na 21.

Sai dai binciken ya ce abin ba haka zai kasance ba a Nahiyar Afirka, inda za a samu ƙaruwar jama'a kusan ninki uku na abin da ake da shi a yanzu nan da shekara ta 2100.

Yawan al'umar Najeriya zai iya kai wa miliyan 800, abin da zai sa ta zama ta ƙasa ta biyu a yawan al'umma a duniya bayan Indiya.

A cewar binciken, ƙasashe irin su Spain da Italiya da Poland da Japan da kuma Thailand za su fuskanci raguwa a yawan al'umarsu da kusan rabi. Hatta China za ta rasa kashi 25 cikin 100 na jama'arta.

An bayyana ƙarancin ilimi ga mata da kuma yawan amfani da ƙwayoyin hana ɗaukar ciki a matsayin manyan dalilan da za su jawo hakan.

Hakan ba siyasar duniya kaɗai zai shafa ba, wajibi ne ƙasashe su yi duba na tsanaki game da tsarin ci-rani da haraji da kuma tsarin kula da yara.

Ganin cewa 'yan sama da shekara 80 za su fi 'yan ƙasa da shekara 5 yawa, wajibi ne kuma a samar da hanyoyin kula da dattijai fiye da na baya.

BBC ta yi nazari kan yadda yawan 'yan Najeriya da za a samu a nan gaba ka iya zame wa kasar damuwa ta fannin tattalin arziki.

'Tasirin hakan ga tattalin arziki a Najeriya

Irin wadannan hasashe idan aka bayar mutane na ganin kawai rashin gaskiya a ciki, amma sam ba haka abin yake ba domin ana duba yanayin karuwar al'ummar kasar ne kowacce shekara wajen fitar da irin wannan hasashe, a cewar Dokta Isa Abdullahi na Jami'ar Kashere a Najeriya.

Dokta Isa wanda kwararre ne a fanin tattalin arziki, ya ce Najeriya na fuskantar koma baya a fannin ci gaba ga shi al'ummarta ba raguwa suke ba, sannan shugabannin ba su fiye bijiro da ayyukan da za su amfani al'ummar da ke tasowa ko wadanda za a haifa a nan gaba ba.

Dokta Isa ya ce idan Najeriya ba ta tashi haikan an samu shugabanni masu adalci da hangen nesa ba, to nan gaba za a tsunduma cikin matsananci hali.

"Har yanzu ba ma iya yi wa kanmu komai, komai shigo da su ake, babu batun bunkasa masana'antu don haka idan muka yi sake har aka zo wannan gabar to rayuwarmu za ta galabaita.

"An lalata gonaki, a da Najeriya ba ta shigo da abinci amma yanzu ana shigo da shi, tufafi ma sai an shigo da su, kusan ba mu da wasu kwararan abun nunawa."

Ana hasashen karuwar jama'a ne don a ja hankulan kasashe su zage damtse su shirya tunkarar abubuwa da ke tafe a nan gaba, kuma rashin shiri na jefa kasa cikin galabaita, a cewar Dokta Isa.

"Najeriya na karuwa ne da kusan kashi 3 cikin 100 na al'ummarta a duk shekara, akwai bukatar mu yi tattalin arzikimu, mu rage dogaro da man fetur a fito da tsare-tsaren gina talakawa da mutane da ke da fasaha da kimiyya.

"Najeriya na da dimbin ma'adinai da za ta iya inganta su, akwai bukatar a samar da tubali tun yanzu domin a samu karuwar tattalin arziki da kuma sake habaka asusu kudaden ajiya.

"Bunkasa noma na daga cikin abin da ya kamata a mayar da kai, idan aka lura a baya darajar dala da yadda take a yanzu akwai bambanci sosai."

Akwai mafita?

Kasashe irinsu Burtaniya na amfani da baki wajen habaka yawan al'ummarsu wanda hakan ke maye gurbin gibin raguwa da ake samu a fannin haihuwa.

Ko da yake wannan ba maslaha ba ce, ganin cewa kowacce kasa ma a duniya yawan al'ummarta na ja da baya.

"Za mu kai matsayin da bude kofofin iyakoki za su kasance tilas ko kuma ya zama gasa, saboda zai kasance mutane sun yi karanci," a ra'ayin wani kwararren mai bincike Ferfesa Christopher Murray a zantawarsa da BBC.

Wasu kasashe sun yi kokarin gwada wasu tsare-tsare kamar inganta tsarin hutun haihuwa ga mata da maza, ba da kula ga yara kyauta, taimakon kudin da samun damar ayyukan yi, sai dai hakan ba ya tasiri.

Sweden ta yi kokarin habaka yawan haihuwar da ake samu a kasar daga kashi 1.7 zuwa 1.9, amma sauran kasashe da suka dage wajen dakile faruwar haka babu wani sauyi da aka gani. Singapore har yanzu alkaluman jarirai da ake haifa na kan kashi 1.3 cikin 100.

Shi kuwa, Dokta Isa na cewa ita ma Najeriya ta rungumi tsari irin na Jamus tun da wuri wajen rage dogaro kan abu guda don tabbatar da cewa al'umma masu tasowa ko wadanda za a haifa nan gaba an yi musu kyakkyawan tanadi.

Sharhi

Wasu na iya cewa haihuwa biyu - wato kowane iyaye su haifi yara biyu, saboda yawan jama'a ya tsaya yadda yake.

Sai dai duk da irin ci gaba ko ingancin fannin lafiya, ba kowanne yaro ke rayuwa har shekarun girma ba.

Kasashen da ke da yawan samun mace-macen kananan yara su ma akwai bukatar a samu karuwa wajen haihuwa.

Abin tambaya ana shi ne ina batun kiraye-kirayen baya da masana suka rinka yi da kwararru kan kayyade iyali?

Farfessa Ibrahim Abubakar na Jami'ar UCL da ke Landan, ya ce: "idan wannan hasashe ko rabinsa ya zama gaskiya, kwararar baki za ta zama tilas ga duk kasashe ba batun zabi.

"Idan muna son nasara to wajibi mu sake tunani kan siyasar duniya.

"Rarraba shekarun aiki a al'umma zai kasance mai muhimmanci ko da za a samu wanzuwa ko akasin haka."