Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
George Floyd: Sabbin bayanai sun nuna yadda 'yan sanda suka hana shi ihu yana kakarin mutuwa
Dan sandan Amurka da ake zargi da kashe George Floyd ya umarce shi ya daina magana lokacin da yake kokuwa da numfashi bayan ya danne masa wuya, a cewar bayanan takardun kotu.
Bakar-fatar ya yi kuka sosai kuma ya rinka ambatar sunan mahaifiyarsa da ta rasu, da 'ya'yansa yana cewa dan sandan Minneapolis zai kashe shi, kamar yadda aka ji a bidiyon da aka nada.
Lauyoyin daya daga cikin jami'an 'yan sandan hudu da ke fuskantar wannan tuhuma ne ya shaida wa Kotu hakan.
Bayanan da takardun ke kunshe da su sun nuna karara ainihin abin da ya faru a wancan lokacin da suka zama na karshe ga Mista Floyd. Mutuwarsa a watan Mayu ta ta da yamutsi a duniya.
Mutuwar Floyd ta haddasa zanga-zangar adawa da wariyar launin fata, wanda kungiyar da ke fafutikar kare hakkin bakar-fata ta jagoranta da takenta - Black Lives Matters movement, a Turance - hakan ya haifar da zazzafar muhawara da tunasar da tarihin Amurka a duniya kan bautar da bayi da raba iyalai.
Dukkanin 'yan sanda hudu da ake zargi da hannu a kisan Mista Floyd an koresu daga aiki tare da garkame su.
Derek Chauvin dan sanda da ya yi amfani da guiwarsa wajen danne wuyar Floyd, na fuskantar tuhume-tuhume da dama ciki harda laifin kisa, yayinda sauran uku - Thomas Lane da J Aleander Kueng da Tou Thao - ana zarginsu da taimakawa wajen aikata kisan.
An fitar da wadanan bayanai ga al'umma a ranar Alhamis bayan lauyan Mista Lane ya bukaci kotu ta yi watsi da karar da aka shigar a kansa.
Gargadi: wasu daga cikin bayanan da za a karanta na iya tada hankali.
Me ke kunshe a cikin takardun?
Kawo yanzu dai, hotunan da shaidu ke yadawa a kafar sada zumunta sun nuna akasarin abin da aka sani akan Mista Floyd daga lokacin kama shi har zuwa mutuwarsa.
Sabbin tarkardun na kunshe da sabbin bayanai daki-daki, Karin haske kan muhimman bangarori, daga lokacin da Mista Lane da Mista Kueng suka iso inda abin ya faru, har zuwa lokacin da aka dauke shi a motar gaggawa aka yi kokarin ganin ko yana sauran numfashi.
Bayanan bidoyon da aka nada daga camerorin da ke makale a jikin Mista Lane da Mista Kueng sun nuna Mista Floyd ya na ambato baya iya numfashi sama da sau 20, sakamakon karfin danne shi da aka yi a titin Minneapolis.
'Yan sandan sun tunkare shi a wajen wani kanti da aka yi zargin wai ya yi amfani da takardar kudin jabu na dala 20 wajen sayan sigari.
A lokaci guda aka iske Floyd sanye da ankwa, an makureshi a kasar titi kusa da motar 'yansanda inda ya yi ta kokuwa da numfashi, yana cewa: "Kai za fa ku kashe ni".
Mista Chauvin, wanda hotuna suka nuna shi lokacin da ya durkusa akan wuyan Mista Floyd na kusan dakika 8, ya amsa shi yana cewa: "Sai ka daina Magana, ka daina ihu. "Magana tana karar da numfashi."
Bayanan da aka shigar a kan takarda sun nuna cewa da farko Mista Floyd ya bada hadin-kai, lokacin da aka kama shi, ya yi Kokorin neman afuwa, yana ta bai wa 'yansandan hakuri lokacin da suka doshi inda ya ajiye motarsa.
Mista Lane ya umarci Floyd ya miko hannusa akalla sau 10, kafin daga bisani ya umarce shi ya fito daga motarsa.
Lokacin da ya amsa bukatar mika hannusa a gani, Mista Floyd ya na mai cewa: "Ka ga, na samu, na samu harbi a irin wannan yanayi, Yallabai, kafin," Ba a fahimci abin da yake nufi ko kokarin cewa ba.
An kai matakin da Mista Lane yake cewa: "Me yasa yake zazzamewa ne kuma ya ki nuna mana hannusa, sannan yana wasu irin abubuwa?"
Dansanda ya sa wa Mista Floyd ankwa da kuma kokarin shigar da shi bayan motarsu.
Lokacin da suka yi kokarin aikata hakan, Mista Floyd ya dimauce, yana ta nanata roko da sanar dasu cewa yana tsoron killacewa.
Mista Lane ya tambashi shi ko "yana da wani abu ne". Mista Floyd ya amsa: "Ina da tsoro, yallabai."
A cewar wasu takardun bayanai na daban, Mista Lane ya shaidawa masu bincike lokacin da aka sa shi cikin mota, Mista Floyd ya yi ta "buge-gube".
Nan take jami'an suka fito da shi daga motar, sannan suka kai shi kasa. Suka makure shi a kas, a cewar takardar bayanan, Mista Floyd ya yi ta kuka babu adadi: "Mama."
Ya ce: "Mutumin ya bani mamaki fa, Mama, ina son ki, ina son ki. "Ku fadawa yara na ina kaunarsu. Na mutu."
A wannan lokacin, Mista Floyd ya ci gaba da roko har numfashinsa ya dauke baki daya, Mista Lane ya tambayi Mista Chauvin: "Mu jefar da shi a gefen titi?"
Dan sanda ya mayar da martani: A'a, mu bar shi a inda muka ganshi kawai."
Lauyan Mista Chauvin bai ce kala ba akan takardun bayanan da aka fitar ba.
Yaushe takardun bayanan za su fito?
An fitar da takardun da ke kunshe da wadannan bayanai ne domin taimaka wa wajen watsi da tuhumar aikata laifi da ake yi wa Mista Lane, wanda sabon jami'i ne da ya kama aki ba jimawa, sai gashi mutuwar Mista Floyd ta faru a hannusa.
Lauyan Mista Lane, Earl Gray wanda ya shigar da wadanan bayanai, ya yi korafin cewa "babu adalci ko hujjar" da za ta kai ga wanda yake karewa ya tsaya gaban kotu don fuskantar tuhuma.
Sabbin takardun kotun sun kunshi bayanan tattaunawar da aka yi da Mista Lane da masu bincike daga Cibiyar binciken laifuka ta Minnesota.
A tattaunawar, Mista Lane ya soma ne da bayanai kan abubuwa da suka faru a dakikokin farkon haduwarsu da Mista Floyd.
Mista Lane ya ce ya ciro bindigarsa sannan ya umarci Mista Floyd ya nuna masa me ke hannusa lokacin da ya doshi motarsa kuma ya gan shi "zaune da hannusa boye a kasar kujera".
Hotunan cikin motar Mista Floyd sun nuna shi zaune kafin a kama shi dauke da takardun kudi na dala 20, wanda Mista Gray ke ikirarin na jabu ne.
A karshen tambayoyin, daya daga cikin masu binciken ya tambayi Mista Lane ko a ransa yaji shi ko Mista Chauvin sun taka rawa wajen mutuwar Floyd.
"Ban yarda da hakan ba. Ba zaka amsa wannan ba kenan," a cewar Gray.
Me ya faru tun bayan mutuwar Mista Floyd?
Faruwar al'amarin da fitowar hotunan bidiyo sun sake fallasa da fama ciwon da mutane ke rike da shi kan nuna wariya da bambanci a Amurka.
Ga wasu mutane da dama, fusatar da aka yi kan mutuwar Floyd ta fito da yawan shekarun da aka kwashe ana nuna kyama da wariya kan lamuran cigaban rayuwar bakar-fata.
Wannan yanayi ya ballo zanga-zangar da har yanzu ba a daina ba a biranen Amurka da sauran kasashe ne ketare.
Jami'an 'yansanda da gwamnatoci da kuma 'yan kasuwa sun nuna bukatar kawo sauye-sauye kan wariya da nuna bambanci ga launin fata wanda hakan ne ya ingiza bore.
An sake waiwaye kan kayayyakin tarihi da ke da alaka da bautarwa da bakar-fata a Amurka da sauran kasashe. An tunbuke wasu ko lalatasu, wasu kuma mahukunta ko cibiyoyi sun umarci a cire su.
Mutuwar Mista Floyd ta biyo bayan shari'ar da ake kan Michael Brown a ferguson, Missouri; Eric Garner a New York; da dai sauran batutuwa da suka asasa kafa ko bijiro da kungiyar kare hakkin bakar-fata wato Black Lives Matter a turanci, a 'yan shekarun nan.