Coronavirus a duniya: Yadda Covid:19 za ta sauya yadda ake aiki

    • Marubuci, Daga Eva Ontiveros
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Bullar annobar korona ta samar da sauyi mai yawa ga yadda miliyoyin mutane ke aiki, daga kara mayar da ayyuka kai tsaye daga intanen zuwa zaman kashe wando da kuma rasa ayyukan yi.

A watan Afirilu kawai mutum miliyan 122 ne suka rasa ayyukansu a Indiya.

Yayin da kasar ke ta neman gano yadda rayuwa za ta kasance bayan dokar kulle, sabbin dabaru kan yadda za a samar da ayyukan yi da kuma tunanin a ina za a samar da su da kuma yaushe za a samar da su na ta bullowa.

"Wannan annobar za ta samar da wani sabon tsari na tunani kan yadda mutane za su hadu su rika aiki tare," in Dakta Mariam Marra, wata malama a kwalejin nazarin kasuwanci ta Henley.

"Za kaga yadda tuni ake magnar komawa aiki na sa'o'in kadan da mutanen da za su rika zuwa aiki a zahiri."

Kasashen New Zealand da Canada da kuma Finland sun ba da satar amsar tsarin aiki anan gaba zai kasance na 'yan sa'o'i kadan da kuma yadda neman aiki zai zamo abu mai sauki.

Sauyin yadda muke aiki zai iya samar da karin damar aiki tukuru, za a kaucewa korar mutane daga aiki, za mu samu cikakken lokacin da za mu rika bibiyar lafiyarmu, da jin dadin rayuwarmu.

Sai dai an yi gargadi kan wasa da wannan gwaji lokacin da wasu kamfanonin ke neman durkushewa saboda koma bayan tattalin arziki.

Rage yawan aiki

Idan za mu yi tunanin yadda muke aiki, watakila za mu iya tunanin na iya wanne lokaci muke bukatar mu yi aiki.

Dakta Marra ta shafe kusan shekarar da ta gabata wurin tattara bayanai daga masana'antu kusan 250 a Burtaniya domin komawa tsarin aiki na kwana hudu a mako, ko dai ta hanyar rage yawan aikin ko kuma ta hanyar yage sa'o'in da ake debewa a lokacin aiki.

"Kuma zai kasance ana biyan albashi cikakke, ko kuma ya zama aiki na wucin gadi," in ji ta.

Ta gano cewa wadannan kamfanoni za su iya samun rara ta a kalla fam biliyan 104 ta hanyar karuwar ayyuka tare da bunkasa lafiyar ma'aikatansu".

Amma wasu na ganin ayi aiki na sa'o'i kadan a mako zai rika lakumewa kamfanonin makudan kudade.

Aiki ta intanet

Yayin wannan annoba kamfanoni sun dogara ne ta hanyar amfani da fasaha ba kawai don haduwa da abokan huldarsu ba harma da tsarawa ma'aikata yadda za su yi aiki.

Ga ma'aikata da yawa a wuraren da ke da karfin tattalin arziki - yadda za a rika aiki a gaba " zai sanyta mutane da yawa zama a gida, da kuma aiki ta intanet da karancin bukatar ofis-ofis," in ji farfesa Hamermesh.

"Hakan baya nufin yin aikin yadda ya kamata da inganci da kuma kyan aiki zai ragu ko kuma zai lalace," in ji Dakta Marra.

Aiki daga kiga akwai wuya akwai dadi ga Tatty.

"Zan iya rungumar tsari koyo daga gida, amma na rasa mu'amalar da nake yi ta zahiri da dalibaina," in ji ta.

Aiki cikin kwanciyar hankali

Mutanen da ke aiki a wurare kamar kantuna da asibitoci da kuma gonaki ba za su iya aiki ta intanet ba, amma da bullar wannan cuta ya haifar da matukar damuwar kamuwa da ita.

"Amma ga wadanda ke son yin aiki yadda ya kamata, ba da tazara ita ce hanyar da ya kamata su bi," kamar yadda Dakta Marra ta bayyana.

"Ba zai yiyu a dawo aiki da yawa ba kamar yadda muke yi a baya."

Wata mafitar kuma ita ce rarraba mutane zuwa lokuta daban-daban da kuma samar musu da lokutan aiki, domin rage wayan mutane da ke shiga ofishi a ko wanne lokaci.

Amma akwai wasu kalubale da masu son shakatawa da kuma wuraren nishadantarwa ke fuskanta. Tabbatar da tazara a dakunan kallo da kuma wuraren kida na nufin yawan mutanen da za su shiga ba za su bayar da kudin da ake bukatar hadawa ba.

Kudaden da kowa ke samu

Watakila mafi yawan sauyin da za a samu anan gaba a wuraren aiki ba akan "ina ne" ko kuma "ta yaya" za mu rayu ba ne, akan menene za a rika biyanmu ne.

Masanin tarihi Rutger Bregman ya ce wannan lokaci ne da zamu rika bai wa mutane kudi. Ba wai a matsayin taimako ba a'a a matsayin abin da suka can-canci samu."

Tafiyar da lokaci wajen yawon bude ido

"Samun wata ranar da babu aiki a cikin mako na karawa mutane kwarin gwiwar su je siyayya, ko wajen cin abinci akai-akai, tare da zuba kudaden cikin kasuwanci da yawa," in ji Dakta Marra a matsayin hujjar binciken da ta yi.

A New Zealand Firaiminista Jacinda Arden ta shawarci shugabannin kamfanoni da su zama masu tafiya da lokaci, su rungumi tsarin aiki kadan a cikin mako ko zai taimaka wajen habbaka yawon bude ido.

Al'amura sun sauya

Mutum zai iya mamaki kan sauyin tsarin aikinmu mai matukar takurawa, amma tarihi zai iya sauya hakan.

A lokacin juyin-juya halin masana'antu, a shekarun 1890, ma'aikata suna aikin kwana shida cikin kwana bakwai kuma ana sa ran su yi aiki na tsawon sa'a 100.

An saba da yin aiki na kwana a biyar a ko ina a duniya, amma da alama hakan ma na iya sauyawa.