Fafaroma ya ce ba za a kara lullube batun cin zarafi a coci ba

Fafaroma ya ce ba za a kara lullube batun cin zarafi ta hanyar lalata tsakanin limaman coci da kananan yara ba a wani yunkuri na rage abin da ke faruwa a coci-coci.

A baya-bayan nan ne fadar Vatican ta yaye labulen zarge-zargen cin zarafi ta hanyar lalata, a matakin da ta ce tana dauka na bai wa wadanda lamarin ya shafa kariya da tsare mutunci.

Sai dai sabbin bayanan da Fafaroma ya fitar a ranar Talata sun zo da mamaki, inda aka dage batun sakaya sunan wadanda suka kawo rahoton zargin cin zarafin, ko suka ce abin ya shafe su.

Shugabannin coci-coci ne dai suka bukaci daukar matakin a taron koli da fadar Vatican ta jagoranta a watan Fabrairun 2019.

Sun yi amanna matakin zai sanya a yi adalci ga wadanda aka ci zarafi da kuma wadanda ake zargi, zai kuma bai wa 'yan sanda da sauran hukumomi samun bayanai a lokacin gudanar da aikinsu.

Har yanzu ana korafi kan rashin samun bayanan da suka dace a lokacin binciken zargin cin zarafi a fadar Vatican.

A sanarwar da Fafaroman ya fitar ya ce a bai wa jami'an fadar Vatican umarnin su bai wa masu bincike hadin kai a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Har wa yau, Fafaroma ya sauya shekarun da ake ganin an ci zarafin yara ta hanyar lalata, inda ya ce duk yaron da aka yi lalata da shi daga shekara 14 har zuwa 18 cin zarafi ne.

Archbishop na Malta Charles Scicluna, wanda kwararre ne kan binciken cin zarafi, ya yaba wa matakin da ya kira mai matukar muhimmanci.