
Kan iyakar Turkiyya da Syria
Majalisar dokokin Turkiyya ta bada iznin gudanar da ayyukan soji a ƙasar Syria dake maƙwabtaka, bayan wani harin roka da aka ƙaddamar daga Syrian, wanda yai sanadiyyar mutuwar Turkawa biyar.
Yanzu dai ƙudurin dokar ya baiwa gwamanti iko na shekara guda, tayi amfani da dakarunta akan tsallaken iyaka, idan har hakan ya zama wajibi.
Tuni dai Turkiyya ta maida martani game da harin na ranar laraba da aka kai akan ƙauyen Akakale dake ƙasar, inda ta harba makaman atilare akan Syria cikin dare.
Sai dai mataimakain Prime Ministan Turkiyyan yace ƙuri'ar da 'yan majalisar suka ƙada na amincewa da buƙatar tura sojojin, ba wai tana nuna za a tafi yaƙi ba ne.
Kuma mataimakin Prime ministan na Turkiyya yace, tuni Syria ta nemi afuwa dangane da abinda ya faru, kuma yace, duk matakin da zasu dauka zai zama da haɗin gwiwar majalisar ɗinkin duniya.
Ɓangarorin biyu dake maƙwabtaka da juna dai sun daɗe ba sa ga maciji.
Turkiyya dai ta sha fitowa fili tana nuna adawa da gwamnatin Syria take murƙushe masu yi mata tawaye.
















