
Shugabar hukumar kula da hada-hadar kasuwar hannun jari a Najeriya-Arunma Oteh
Majalisar wakilan Najeriya ta bai wa shugaban kasar wa'adin makwanni biyu da ya sauke shugabar hukumar da ke kula da hada-hadar kudin kasar, Miss Arunma Oteh daga mukaminta ko su dauki mataki a kansa.
Majalisar ta bayyana matakin da bangaren shugaban kasar ya dauka na maida shugabar hukumar kan mukaminta da cewar bai dace ba, tana zarginsa da rashin martaba kudurce-kudurcen majalisar.
Kimanin watanni biyu da suka wuce ne wani kwamitin majalisar ya ba da shawarar a sauke shugabar daga mukamin nata bisa zargin cewa ba cancanci rike mukamin ba.
Majalisar wakilan Najeriyar ta cimma matsayar tata ne a zamanta na farko bayan dawowar 'yan majalisar daga wani dogon hutu na kimanin watanni biyu, inda baki dayan'yan majalisar suka yi ittifaki cewa matakin da bangaren zartarwar kasar ya dauka na mai da shugabar hukumar da ke sa-ido a kan hada-hadar kudi da hannayen-jarin kasar Ms Arunma Oteh kan mukaminta bai dace ba.
Hasali ma 'yan majalisar cewa suka yi yadda shugaban kasar ya dauki matakin a daidai lokacin da kwamitin majalisar ya tattabatar da bincikensa da matsayin cewa a kori shugabar tamkar cin-fuska ne ga majalisar.
















