
Kudin Najeriya
Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar da Babban Bankin kasar daga shirinsa na fitar da sabuwar takardar kudi ta N5000, da kuma mayar da wasu takardun kudin sulalla.
Majalisar ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda babban bankin bai gabatar mata da batun ba kamar yadda dokar da ta kafa shi ta yi tanaji.
Sanata Isa Galaudu shi ne mataimakin shugaban kwamatin harkokin kudi da inshora na Majalisar ya shaidawa BBC cewa shirin zai haddasa hauhawar farashin kayayyaki da kuma karfafa cin hanci da rashawa a kasar.
A cewarsa, Babban Bankin zai sanya 'yan Najeriya su kara shiga cikin mummunan halin tattalin arziki saboda kudin kasar zai kasance mara daraja a kasuwanni.
A makon jiya ne Babban bankin Najeriya ya ba da sanarwar cewa zai fito da sabuwar takardar kudi ta naira dubu biyar a cikin jerin kudaden kasar da ake hada hadar kasuwanci da su.
Babban Bankin ya ce sabuwar takardar kudin da ake shirin fitowa da ita a shekara mai zuwa za ta kasance dauke ne da hoton fuskokin wasu fitattun mata uku a Najeriya wato Margaret Ekpo da Hajia Gambo Sawaba da kuma Funmilayo Kuti.
Babban Bankin ya ce, a yanzu za a sauya wa takardun kudi na naira 50, da naira 100, da naira 200, da naira 500, da naira 1,000 fasali, sannan a samar da sabuwar naira 5,000.
Kananan kudi da suka hadar da naira 5, da naira 10, da naira 20 kuma duk za a mayar da su tsaba.
Bankin na CBN din dai ya jaddada cewa yana kuma da burin kara inganta yanayi da fasalin kudaden da ake da su, domin kara musu karfi da daraja da kuma tsaro.
















