...Daga Bakin Mai Ita tare da Abale

Bayanan bidiyo, ...Daga Bakin Mai Ita tare da Abale

Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan kashi na 61, shirin ya tattauna da Adam Abdullahi Adam, wanda ake yi wa lakabi da Abale, tauraro a Kannywood.

A wannan shiri ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa da rawar da yake takawa a fina-finai.

Ɗaukar bidiyo: Abdulsalam Usman Abdulkadir

Tacewa: Fatima Othman

Tsarawa da gabatarwa: Buhari Muhammad

Wasu na baya da za ku so ku kalla