...Daga Bakin Mai Ita tare da Musbahu M Ahmad
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.
A wannan kashi na 56, shirin ya tattauna da Musbahu M Ahmad, fitaccen jarumi kuma mawaki a Kannywood.
Musbahu ne ya rera fitattun waƙoƙi irin su Sangaya da Sangdandale.
A wannan shiri ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa ciki har da alaƙarsa da ƴan uwansa biyu da su ma suke masana'antar Kannywood wato Naziru M Ahmad Sarkin Waka da darakta Aminu Saira.
Ɗaukar bidiyo da Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir
Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh