Zaɓen Amurka na 2020: Mutanen ƙauyen Kamala Harris a Indiya na murnar nasararta

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wannan ƙauyen da ke jihar Tamil Nadu a kudancin Indiya nan ne asalin garin da aka haifi kakan Kamala Harris na wajen uwa.

Mazauna wajen a yanzu suna ta murnar nasarar da ta samu a zaɓen Amurka ta hanyar yin wasa da tartsatsin wuta da rarraba alawa.

An kuma lilliƙa hotunan Harris ta ko ina a ƙauyen Thulasendrapuram, sannan an yi addu'o'i a wajen ibada na addinin Hindu.

Harris ce mace ta farko kuma baƙar fata daga yankin Asiya da ta zama mataimakiyar shugaban ƙasa a tarihin Amurka.

Ƙarin wasu labaran