Bidiyo: Trump ya yi zargin an yi masa maguɗin zaɓe tun sakamako bai kammala ba

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Duk da cewa akwai miliyoyin ƙuri'un da ba a kammala ƙidayawa ba a zaɓen Amurka, Shugaba Donald Trump ya yi da'awar lashe zaɓe ba tare da wata hujja ba.

Ya kuma yi zargin cewa an tafka maguɗi tare da ha'intar ƙasarsa ta Amurka.

Don haka ya ce zai garzaya Kotun Ƙoli don ƙalubalantar sakamakon.