Zaɓen Amurka Na 2020: Bidiyon yadda aka yi wa Trump ihun 'ba ma yi' a Kotun Ƙolin Amurka

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Dandazon jama'a a harabar Kotun Ƙolin Amurka sun yi ta yi wa Shugaba Donald Trump ihu da sowar ''kar ku zaɓe shi.''

Ya ziyarci kotun ne a ranar Alhamis da safe don nuna girmamawarsa ta bakwana ga marigayiya mai shari'a Ruth Bader Ginsburg.

Trump ya ƙagara ya maye gurbin Ginsburg kafin zaɓen 3 ga watan Nuwamba na shugaban ƙasa - abin da ƴan Democrats ba sa so.

Tun da farko a ranar Alhamis manyan 'yan jam'iyyar Republican sun bayyana cewa jam'iyyarsu za ta karɓi sakamakon zaɓen shugaban ƙasa duk yadda ya fito.

'Yan jam'iyyar sun bayyana hakan ne bayan da Donald Trump ya ƙi bayyana matsayarsa kan ko zai miƙa mulki cikin ruwan sanyi ko kuma akasin hakan.

Shugaban Jam'iyyar Republican a Majalisar Dattawan Ƙasar Mitch McConnell ya bayyana cewa za a rantsar da wanda ya ci zaɓen a watan Janairu.

Ya bayyana cewa za a bi tsari wurin rantsar da wanda ya ci zaɓen kamar yadda aka saba a duk bayan shekara huɗu, kamar yadda aka fara hakan tun a 1792.